'Yan bindiga sun kai hari ofishin gidan jarida a Abuja, sun yi barazanar kashe ma'aikata baki ɗaya

'Yan bindiga sun kai hari ofishin gidan jarida a Abuja, sun yi barazanar kashe ma'aikata baki ɗaya

  • Wasu 'yan bindiga sun kutsa harabar gidan jaridar ThisDay da ke birnin tarayya a Abuja cikin dare sun yi wa ma'aikata barazana
  • Masu gadin gidan jaridar sun tabbatar da lamarin inda suka ce maharan sun ci mutunci wani ma'aikaci daya, sannan suka yi wa saura barazana cewa za su kashe su
  • Kawo yanzu dai ba a san dalilin da yasa maharan suka yi kutse a gidan jaridar ba amma tuni an sanar da yan sandan afkuwar lamarin kuma sun fara bincike

Abuja - Wasu dandazon yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kutsa ofishin jaridar ThisDay da ke Utako a birnin tarayya Abuja a daren ranar Alhamis kuma suka yi barazanar kashe ma'aikata.

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigan sun haura katanga ne suka kutsa harabar kamfanin cikin dare.

Kara karanta wannan

Hukumar shige da fice ta dakile yunkurin safarar mutum 189, ta yi ram da wadanda ta ke zargi

'Yan bindiga sun kai hari ofishin gidan jarida a Abuja, sun yi barazanar kashe ma'aikata
'Yan bindiga sun afka ofishin ThisDay a Abuja, sun yi barazanar kashe ma'aikata. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar jaridar, yan bindigan, kawo yanzu ba a san dalilin da yasa suka yi kutsen ba misalin karfe 3 na daren Alhamis.

Rahoton da jaridar ta fitar ya ce:

"Duk da cewa har yanzu ba a san dalilin da yasa yan bindigan suka kutsa harabar mu ba misalin karfe 3 na daren Alhamis, masu gadin da ke aiki a ranar, sun ce yan bindigan sun rika cin zarafin wani ma'aikaci, suka kuma yi barazanar kashe dukkansu idan suka sanar da yan sanda."

Amma, yan bindigan sun fice daga harabar kamfanin bayan misalin mintuna 45 suna razana ma'aikatan suka kuma yi sha alwashin cewa za su dawo nan ba da dadewa ba, rahoton Daily Trust.

Jaridar ta kara da cewa mahukunta tuni sun kai rahoton faruwar abin a hedkwatar yan sanda da ke Utako a Abuja.

Kara karanta wannan

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe rai 1, sun tasa ƙeyar mutum 15 cikin daji

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel