Hukumar shige da fice ta dakile yunkurin safarar mutum 189, ta yi ram da wadanda ta ke zargi

Hukumar shige da fice ta dakile yunkurin safarar mutum 189, ta yi ram da wadanda ta ke zargi

  • Hukumar shige da fice ta Najeriya reshen jihar Legas ta dakile yunkurin safarar yara mata da maza 189 a jihar Legas
  • Baya da haka, hukumar ta yi ram da wadanda ake zargin za su fitar da yaran da sunan za a kai su karatu kasashen ketare
  • Sai dai bincike ya nuna cewa, babu takardar shaidar samun gurbin karatun kuma babu takardun tafiya a tare da su

Legas - Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS), rundunar sintiri ta iyakar Jihar Legas a Seme da ke Badagry, ta kama yara 189 maza da matan da ake zargin ana yunkurin safarar su.

Wadanda aka kaman a cewar su an dauka nauyin karatun su ne kuma za su Jamhuriyar Benin, amma sai dai ba a ga takardun tafiyar ba, shaidar samun gurbin karatu da shaidar daukan nauyin su a tare da su ba, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja

Hukumar shige da fice ta dakile yunkurin safarar mutum 189, ta yi ram da wadanda ta ke zargi
Hukumar shige da fice ta dakile yunkurin safarar mutum 189, ta yi ram da wadanda ta ke zargi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An gano yadda aka kama yaran masu kananan shekaru, wadanda ba za su wuce daga shekara 15-20 a cikin kwana 2. Sai dai an dakatar da 92 daga ciki a iyakar a ranar Asabar, sauran kuma an kama su ne a ranar Litinin.

An gano yadda wata coci wadda ake wa lakabi da faith- based institution ta dauko yaran, wadanda suka kun shi mata 115 da maza 74 yayin da wasu daga cikin fastocin su suka musu jagora.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai rikon kwaryar shugaban hukumar kula da shige da ficen, Isah Jere Idris, ya bayyana yadda aka kama yara mazan a shiyya ta farko a hedkwatar da ke Legas a ranar Talata.

Bincike ya bayyana wadanda aka kaman 'yan jihohin Abia, Kogi, Anambra, Akwa Ibom, River, Legas da Jihar Imo da sauran su ne, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Zamfara: An gurfanar da dillalin motocci kan zargin cin 'sassan jikin yaro' ɗan shekara 9

Kakakin hukumar, Amos Okpu, a wata takarda, ya ce binciken ya bayyana yadda aka kama wani Sunday Emmanuel Chinasa da wata Rose Onum Uduma yayin da suka jagoranci tafiyar.

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe rai 1, sun tasa ƙeyar mutum 15 cikin daji

A wani labari na daban, 'yan bindiga masu tarin yawa sun kai farmaki karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, a wannan karon sun sheke mutum 1 yayin da suka yi garkuwa da sauran mutanen kauyen guda 15, wadanda yawancin su mata ne.

Channels TV ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan kamar yadda aka bada labari sun kai farmaki kauyen Batagari a yankin Maikujeri na karamar hukumar, yayin da suka bayyana a kan babura.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, sun iso kauyen ne yayin da suka yi ta harbi a iska dan su jefa firgici a zukatan mazauna kauyen.

Majiyoyi daban-daban sun bayyana yadda 'yan ta'addan bayan sun razanar, suka fara yawo daga gida zuwa gida suna bincikar kowanne lungu da sako suna kwasar muhimman kayayyakin mutane.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel