Landan zuwa Zamfara: Lokuta 10 da jirgin Buhari ya fasa zuwa wata kasa ko gari a mintin karshe

Landan zuwa Zamfara: Lokuta 10 da jirgin Buhari ya fasa zuwa wata kasa ko gari a mintin karshe

  • A yau Alhamis aka ji labari shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fasa kai ziyara zuwa Zamfara
  • Ba wannan ne karon farko da aka shirya tarbar Mai girma shugaban kasar, sai bai samu hallara ba
  • Mun tattaro sauran tafiye-tafiye da Buhari ya fasa ko ya daga da dalilin da suka sabbabba hakan

A wannan rahoton, Legit.ng Hausa ta zakulo manyan tafiye-tafiyen da aka ji shugaba Buhari ya fasa:

1. Ribas (2016)

A watan Yunin 2016 ne Mai girma Muhammadu Buhari ya bada sanarwar ba zai samu halartar bikin kaddamar da aikin share kasar Ogoni ba, sai dai ya aika Farfesa Yemi Osinbajo.

Har yau ba a san dalilin da ya sa shugaban kasar ya fasa wannan tafiya a mintin karshe ba.

2. Legas (2016)

Kara karanta wannan

Farin jinin Buhari, da abubuwa 8 da za su taimakawa Osinbajo a takarar Shugaban kasa

A watan Mayun 2016 Malam Garba Shehu ya bayanna cewa Mai gidansa ba zai samu zuwa Legas ba. A wancan lokaci an yi ta rade-radin cewa shugaban kasar bai da isasshen lafiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Sanagal (2016)

Duk a wannan lokaci ne Muhammadu Buhari ya fasa halartar taron kungiyar ECOWAS da aka yi a kasar Sanagal. A lokacin ya rasa zama na musamman na 49 da aka yi a garin Dakar.

4. Bauchi (2016)

A karo na biyu sai aka ji jirgin Muhammadu Buhari ya fasa zuwa garin Bauchi a Disamban 2016 saboda hazo. A lokacin an sa rai zai kaddamar da wani sabon asibitin sojojin sama.

Jjirgin Buhari
Muhammadu Buhari a jirgi Hoto: www.ft.com
Asali: UGC

5. Nijar (2017)

A karshen shekarar 2017 fadar shugaban kasa ta fito t abayyana cewa Muhammadu Buhari ba zai je Jamhuriyyar Nijar bayan an shirya ganinsa wajen taya kasar bikin samun ‘yancin na 59.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

6. Abia (2018)

Bayan ‘yan kwanaki sai wasu gidajen yada labarai su ka rahoto cewa shugaban kasa ya fasa zuwa gangamin APC a Abia, sai aka ji shi yana ganawa da gwamnan Benuwai, Samuel Ortom.

7. Ruwanda (2018)

Watanni biyu da fasa zuwa jihar Abia, sai kuma shugaban Najeriyar ya kauracewa muhimmin taro a Ruwanda. A dalilin haka Najeriya ta ki sa hannu a yarjejeniyar AfCFTA a lokacin.

8. Edo (2018)

A watan Nuwamban 2018 shugaban kasa ya fasa kai ziyara zuwa jihar Edo, sai aka ji shi a Borno. Ba wannan ne karon farko da aka sa ran ganin Buhari, amma hakan bai yiwu ba.

9. Landan (2021)

Bayan sanarwa ta zo a Yunin 2021 cewa uhammadu Buhari zai je ganin likitansa a Landan. Sai kwatsam Femi Adesina ya fito ya ce an fasa wannan tafiya, ba tare da ya bada dalili ba.

10. Ogun

A karshen shekarar da ta wuce watau 2021, Mai girma Muhammadu Buhari ya fasa zuwa garin Abeokuta. Kwanaki bayan an yi ta surutu, ya ziyarci jihar ya kaddamar da wasu ayyuka.

Kara karanta wannan

AFCON 21: Sanata ba zai ci abinci ba, da martanin jama’a bayan yin waje da Najeriya

Ziyarar Zamfara

Dazu nan aka samu rahoto shugaban kasa ya daga ziyarar da yayi niyyar kai wa zuwa jihar Zamfara domin ya jajantawa al'umma tulin rashin da suka yi.

Gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari ya kirasa a waya domin ya taya shi ba al'ummar jihar ta sa hakuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel