AFCON 21: Sanata ba zai ci abinci ba, da martanin jama’a bayan yin waje da Najeriya

AFCON 21: Sanata ba zai ci abinci ba, da martanin jama’a bayan yin waje da Najeriya

  • Cameroon - A ranar Lahadi, 23 ga watan Junairu 2022, Najeriya ta gwabza da kasar Tunisiya a gasar cin kofin Afrika, inda Super Eagles ta sha kashi da ci 0-1
  • Mutanen Najeriya ba su ji dadin sakamakon wannan wasa ba. Legit.ng Hausa ta tattaro maku martanin jama’a a shafukan sada zumunta bayan tashi wasan

An ji tsohon Sanata Shehu Sani yana kuka, ya na cewa ba zai ci abinci ba sai gobe (Litinin) saboda rashin nasarar da ‘Yan wasan Super Eagles su ka samu

Bayan an tashi wasan Najeriya da Tunisiya babu sa'a, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce ‘yan kwallon kasar sun yi bakin kokarinsu.

“A daren yau (Lahadi), ‘Yan Nigeria Super Eagles dinmu sun yi duk abin da za su iya. Ko da dai mun ci buri, kuma ba mu ji dadin wannan sakamakon ba.

Kara karanta wannan

AFCON: Kocin Najeriya ya fadi babban dalilin da ya sa Tunisiya ta yi waje da S/Eagles

A kwallo, wata rana ka yi nasara, wata rana ayi nasara a kan ka! Ina jinjinawa ‘yan wasanmu, masu horaswa, da wadanda suka bada gudumuwa kawo haka.
#SoarSuperEagles"

- Abubakar Bukola Saraki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Laifin gola ne?

Ya kamata a ce Maduka Okoye ya yi kokari fiye da wannan. Da kyau Umar Sadiq. Koci Eguavoen a ‘yan wasa sun bar AFCON. Sai a tari gaba. Da kyau Super Eagles!

- Hack Emmanuel a Twitter

Shi kuma wani Abba Gwale a shafinsa na Facebook, ya ce:

“Shima wannan golan na Nigeria bai yi kokari ba wajen tare kwallon, ko budurwar sa ai zata iya tare wannan ball din."

- Abba Gwale

AFCON 21
'Yan wasan Super Eagles Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

A'a!

"Mu na daura laifi a kan Okoye Maduka saboda an ci Najeriya. Tun a minti na 47 aka zurawa Super Eagles kwallo a raga. Meya hana Najeriya ta rama a sauran mintunan? A daina wannan maganar, Najeriya ta sha kashi ne saboda ta sha kashi kurum.!

Kara karanta wannan

Baturiya mai auren ‘Dan Najeriya ta rangada ado, ta ci ankon atamfa da yara da mai gidanta

- @IbeawuchiJust1

“Super Eagles: Daga a jira mu ga gudun ruwansu, aka koma cewa za su iya lashe gasar, zuwa mashirmata. Duk a cikin wasanni hudu. Ku yi hakuri ‘Yan Najeriya.”

- Abubakar Adam Ibrahim

Koci ya yi kuskure

Bai kamata a ce kocin ya fara wasa da Chukwueze ba, da ya buga 4-3-3 ne kamar ya yi a wasan Masar. Amfani da ‘yan wasan gaba ta gefe bai aiki da kyau kamar yadda aka gani a wasan Aljeriya a 2019.

- TBQ

Tun shekarar 2001 na ke goyon bayan Arsenal da Super Eagles. Ina tunanin zan zama miji mai hakuri.

- Eliab Ikyiriza

A shafinsa na Twitter, Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmaad ya ce Alkalin wasa ya yi kura-kurai. Amma duk da haka, ya yabawa irin kokarin 'yan wasan.

Da kyau Super Eagles, kun yi kokari sosai, kuma kasarku da mutanenta suna yaba maku. Har abada mu na tare da ku.

Kara karanta wannan

AFCON: Babban Attajirin Afrika, Otedola ya yi wa Super Eagles alkawarin fiye da N100m

- Bashir Ahmaad

Alkalin wasa bai kyauta ba

A baya an ji cewa Kocin Najeriya, Augustine Eguavoen yana ganin jan katin da aka ba Alex Iwobi a filin wasan Roumdé Adjia ya sa aka kori Najeriya daga gasar.

Kocin rikon yana so 'Yan wasan Super Eagles su manta da duk abin da ya faru a kasar Kamaru, su fara shirin fuskantar Ghana domin zuwa gasar cin kofin Duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel