Farin jinin Buhari, da abubuwa 8 da za su taimakawa Osinbajo a takarar Shugaban kasa

Farin jinin Buhari, da abubuwa 8 da za su taimakawa Osinbajo a takarar Shugaban kasa

  • Mun tattaro wasu abubuwan da za su iya taimakawa Yemi Osinbajo a zabe mai zuwa da za ayi a 2023
  • Akwai yiwuwar Farfesa Osinbajo ya nemi ya fito takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC
  • Kusan za a iya cewa farin jinin Buhari ya rabi Osinbajo, sannan bai tara makiya da yawa a kan mulki ba

Ga wadannan dalilai nan kamar haka:

1. Cigaban gwamnatin Buhari

Jama’a musamman magoya bayan jam’iyyar APC za su ga cewa Yemi Osinbajo shi ne na biyun Buhari, don haka shi ne ya fi dacewa ya karbi ragama a 2023.

2. Goyon bayan manyan kasa

Wani rahoto ya bayyana cewa akwai wasu manyan gwamnoni hudu masu-ci da suke kokarin ganin Yemi Osinbajo ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben badi.

Kara karanta wannan

Kaduna 2023: Dattijo, Sanata Uba Sani da ‘Yan siyasa 7 da ke harin Gwamna a APC

Baya ga haka akwai wani Basarake daga yankin Arewacin Najeriya da ake zargin ya tsaya masa. Sannan ana ganin yankin farin jinin Buhari ya yi naso zuwa kan shi.

3. Tikitin musulmi da kirista

Akwai hadari jam’iyyar APC ta tsaida Musulmi da Musulmi (kamar Tinubu), Osinbajo yana cikin wadanda za a ba tikiti hankali kwance ba tare da an ji wani dar-dar ba.

Osinbajo
Farfesa Osinbajo da Shugaban kasa Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

. Kuri’un mabiya kirista

Idan Farfesa Osinbajo ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 2023, ana tunanin zai samu dinbin kuri’u daga mabiya addinin kirista musamman ‘yan cocinsa na RCCG.

5. Babu kazanta tare da shi

Kusan kawo yanzu ba a taba cewa an samu Yemi Osinbajo da wani laifi na rashin gaskiya ba. Osinbajo yana cikin ‘yan takarar da ba su da wani tabo a tattare da su.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

6. Bai taka kowa ba

Duk da Osinbajo ya na cikin gwamnatin Muhammadu Buhari, amma kusan bai yi amfani da kujerarsa, ya taka mutane ba, don haka yake da karancin makiya a siyasa.

7. Sanin kan aiki

Baya ga cewa babu zargin aika-aika da ake yi wa mataimakin shugaban kasar, ana ganin ya fi da-dama daga cikin masu harin kujerar shugaban kasa sanin kan-aiki.

8. Ilmin boko

Idan Yemi Osinbajo ya yi nasarar zama shugaban kasa a zabe mai zuwa, zai zama Farfesan farko da ya jagoranci Najeriya. Baya ga haka babban lauya ne da ake ji da shi.

Cikas a zaben 2023

A baya kun ji cewa akwai wasu katangu da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo yake bukatar ya tsallake kafin ya iya karbar shugabancin Najeriya a 2023.

Duk da wadannan kalubale, Farfesa Osinbajo ya yi dace inda yake da wasu gwamnoni da sarakunan Arewacin kasar nan da suke goyon bayan ya hau mulki.

Kara karanta wannan

Takarar Shugaban kasa: Fito-na-fito da Tinubu, da kalubale 4 da suke jiran Osinbajo a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel