Yanzu-yanzu: Daga Sokoto, Shugaba Buhari ya fasa zuwa Zamfara saboda yanayi ba kyau

Yanzu-yanzu: Daga Sokoto, Shugaba Buhari ya fasa zuwa Zamfara saboda yanayi ba kyau

  • Shugaban kasa ya dage ziyarar da yayi niyyar kaiwa jihar Zamfara a ranar Alhamis
  • Gwamna Matawalle ya bayyana cewa shugaban kasan ya kirasa don ya tayashi baiwa al'ummar jihar hakuri
  • Shugaba Buhari ya yi alkawarin komawa makon gobe amma ba za'a ayyana ranar ba

Sokoto - TVCNews ta ruwaito cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya fasa zuwa jihar Zamfara sakamakon bacin yanayi a sararin samaniya.

Shugaban kasan dai yanzu yana jihar Sokoto kuma zai koma birnin tarayya Abuja.

Buhari ya shirya kai ziyara wajen gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, don jajanta masa bisa rashin rayukan da akayi sakamakon hare-haren yan bindiga.

Shugaba Buhari ya fasa zuwa Zamfara saboda yanayi ba kyau
Yanzu-yanzu: Daga Sokoto, Shugaba Buhari ya fasa zuwa Zamfara saboda yanayi ba kyau Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa Shugaban kasan ya shirya tashi daga Sokoto amma ya fasa saboda lalacewar yanayi, riwayar DailyTrust.

Kara karanta wannan

Bayan dage zuwa Zamfara saboda bacin yanayi, Buhari ya dira Abuja

Matawalle yace:

"Shugaban kasa ya min magana kuma yace in tayashi bada hakuri ga al'ummar jihar nan."
"Shugaban kasa ya ce zai dage zuwansa zuwa makon gobe amma za'a sanar da mu ranar da aka zaba."
"Wasu Hafsoshin tsaro yanzu haka suna Katsina amma sun kasa zuwa hawa jirgi zuwa Zamfara saboda dalili guda."
Muna baiwa al'ummar jihar nan hakuri bisa wannan dage ziyara. Mun godewa shugaban kasa bisa soyayyarsa."

Shugaba Buhari ya kaddamar da manyan ayyuka biyu a Sokoto

Shugaban kasar da safiyar yau Alhamis ya tafi jihar Sokoto inda ya kaddamar da wani sabon kamfanin siminti na tan miliyan uku da kamfanin BUA ya gina.

Buhari ya kuma kaddamar da tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 48 a jihar.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar Gwamnan jihar Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal; Gwamnan bankin CBN, Mr Godwin Emefele; Shugaban kamfanin BUA, Alhaji AbdulSamad Rabi'u, Shugaban kamfanin Max Air, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel