Yanzu-Yanzu: Ma'aikata sun yi zanga-zanga kan daukan sabbin 'yan sanda, sun garkame hedkwatar PSC a Abuja

Yanzu-Yanzu: Ma'aikata sun yi zanga-zanga kan daukan sabbin 'yan sanda, sun garkame hedkwatar PSC a Abuja

  • Ma'aikata sun garkame hedkwatar PSC da ke Abuja bisa samun rahoto akan yadda hukumar ta fara daukar sabbin jami’ai 10,000 aiki
  • Jami’ian sun tilasta sakataren hukumar, William Alo da darektocin fitowa daga ofisoshin su inda suka sanar da yajin aiki na kwana 3 da zai fara daga yau
  • Sun dauki wannan matakin ne saboda daukar sabbin jami’ai da hukumar take ai, rashin karin girma ga ma’aikata da sauran su

Abuja - Ma'aikatan Hukumar Kula da Walwalan Yan Sanda, PSC, sun garkame hedkwatar hukumar da ke Abuja, kan rahoton cewa hedkwatar yan sandan za ta karbe aikin daukan sabbin 'yan sanda 10,000 da PSC ke yi a yanzu, The Punch ta ruwaito.

Hakan yasa jami’an suka kori Sakataren Hukumar, William Alo da sauran darektocinsu daga ofisoshinsu daga nan suka shelanta fara yajin aikin gargadi na kwana uku wanda zai fara daga yau.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Da Duminsa: 'Yan sanda suna zanga-zanga saboda daukar sabbin jami’ai, sun garkame hedkwatar PSC da ke Abuja
Ma'aikata sun yi zanga-zanga a Hukumar Kula da Jin Dadin Yan Sanda, PSC a Abuja. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami’an suna zanga-zanga ne akan yadda hukumar ta fara daukar kananun ma’aikata, rashin yi wa jami’anta karin girma da kuma horarwa.

The Punch ta bayyana rahotanni akan yadda ma’aikatan suka tafi yajin aiki bisa zargin Musiliu Smith, Sifeta Janar na ‘yan sanda mai murabus da sakin kundin tsarin PSC ga ‘yan sanda.

Daukar aiki: Hukumar ‘yan sanda ta saki jerin sunayen wadanda suka yi nasara

A baya, kun ji cewa Hukumar 'yan sanda ta saki jerin sunayen wadanda ta dauka aiki, ranaku, wurare da kuma abubuwan bukata domin horar da sabbin daukar na 2020.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe, a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu, Punch ta rahoto.

Ndukwe ya shawarci wadanda suka yi nasara da su ziyarci shafin daukar ma'aikata na hukumar da ke www.policerecruitment.gov.ng domin samun kwafin jerin sunayen da kuma duba sunayensu ko kuma su ziyarci hedkwatar rundunar ‘yan sandan na jiha don duba jerin sunayen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel