Daukar aiki: Hukumar ‘yan sanda ta saki jerin sunayen wadanda suka yi nasara

Daukar aiki: Hukumar ‘yan sanda ta saki jerin sunayen wadanda suka yi nasara

  • Hukumar 'yan sanda ta fitar da jerin sunayen wadanda ta dauka aiki domin fara atisaye
  • An bukaci wadanda suka nemi aikin da su je shafin www.policerecruitment.gov.ng domin duba sunayensu ko kuma su ziyarci hedkwatar rundunar ‘yan sandan na jiha
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe, a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu

Hukumar 'yan sanda ta saki jerin sunayen wadanda ta dauka aiki, ranaku, wurare da kuma abubuwan bukata domin horar da sabbin daukar na 2020.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe, a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu, Punch ta rahoto.

Daukar aiki: Hukumar ‘yan sanda ta saki jerin sunayen wadanda suka yi nasara
Daukar aiki: Hukumar ‘yan sanda ta saki jerin sunayen wadanda suka yi nasara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ndukwe ya shawarci wadanda suka yi nasara da su ziyarci shafin daukar ma'aikata na hukumar da ke www.policerecruitment.gov.ng domin samun kwafin jerin sunayen da kuma duba sunayensu ko kuma su ziyarci hedkwatar rundunar ‘yan sandan na jiha don duba jerin sunayen.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Zariya, sun kashe mutane

Ndukwe ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Hukumar na fatan sanar da mazauna jihar, wadanda suka nemi aikin 'yan sandan Najeriya na daukar sabbin jami'ai 10,000 na 2020 sannan suka yi nasarar zuwa matakin tantance lafiyarsu cewa sunayen karshe ya fito.
"Jerin sunayen na karshe na kuma dauke da ranaku, wuri da kuma abun bukata na atisaye.
"Wadannan mutane, wadanda suka ga sunayensu a jerin sunayen karshe, su tafi kwalejin 'yan sanda da aka kebe domin horar da sabbin daukan."

Ndukwe ya bayyana cewa wadanda suka yi nasara daga jihar Enugu su tafi kwalejin 'yan sanda na Oji-River, tsakanin 10 ga watan Janairu da 15 ga watan Janairun 2022 domin yin atisaye, inda ya kara da cewar ba za a kwashi wadanda suka yi latti don atisayen ba.

Kakakin yan sandan ya ce wadanda suka yi nasarar su isa kwalejin yan sandan da kayayyaki kamar haka:

Kara karanta wannan

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

"Fararen riga da gajerun wando biyu; fararen takalmar atisaye biyu da safar kafa biyu; fararen rigunan motsa jiki biyu, zanuwan gado farare biyu; rigunan filo farare biyu; takunkumin fuska da abun kashe kwayoyin cuta na hannu.
"Karamin kulan zuba abinci da filet biyu da cokula; fatanya daya, adda da tsintsiya; bokiti daya da kayan bandaki; littafi, da ainahin katin shaidar dan kasa; ainahin takardun makaranta, da hotunan fasfot hudu mai farin bango."

Shugaba Buhari ya amince da daukar ‘yan Najeriya 10,000 aikin ‘yan sanda

A baya mun kawo cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da daukar 'yan Najeriya 10,000 aiki a matsayin jami'an 'yan sanda.

Hakan na daga cikin kokarin gwamnatinsa na magance matsalolin tsaro da suka addabi yankuna daban-daban na kasar.

Kamar yadda mai ba shugaban kasa shawara kan kafofin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce an dauki jami'an ne a fadin jihohi 36 na kasar da babbar birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Bayani: Mazauna unguwa a Legas sun yi zanga-zanga saboda girke musu 'yan sanda

Asali: Legit.ng

Online view pixel