Fadar Shugaban kasa ta tonawa Gwamnan PDP asiri, ta ce ya fi kowa rashin biyan albashi

Fadar Shugaban kasa ta tonawa Gwamnan PDP asiri, ta ce ya fi kowa rashin biyan albashi

  • A ranar Talata 25 ga watan Junairu 2022, fadar shugaban kasa ta fito, ta caccaki Gwamna Samuel Ortom
  • Garba Shehu ya dura kan gwamnan jihar Benuwai, Samuel Orom a kan sukar Muhammadu Buhari da ya yi
  • Mai ba shugaban Najeriya shawara ya ce Ortom bai iya biyan ma’aikatan jiharsa albashi da kudin fanshonsu

Abuja - Fadar shugaban kasa ta dura kan gwamnan Benuwai a dalilin fitowa da ya yi a wani gidan talabijin, ya na mai sukar Mai girma Muhammadu Buhari.

Malam Garba Shehu ya fitar da wani jawabi na musamman wanda ya yi wa take "The Incongruence of Governor Samuel Ortom on Arise TV” a yammacin jiya.

Hadimin shugaban kasar ya ce Ortom yana yawan daura laifi kan Muhammadu Buhari wanda duk da halin da ake ciki, yana biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

A cewar Garba Shehu, a maimakon gwamnan ya biya ma’aikatansa albashi, yana sukar Buhari. Abin na sa har ma ya kai yana cin mutuncin wadanda yake mulka.

Daily Trust ta rahoto Shehu yana cewa gwamnan ya gaza sauke nauyin da ke kansa duk da ya karbi taimako, bashin kudi, da wani aron daga cikin asusun ECA.

Duk da wadannan kudi da gwamnan na Benuwai ya rika karba daga hannun gwamnatin tarayya, bai iya samun yadda zai biya ma’aikata albashi da fanshonsu ba.

Shugaban kasa
Muhammadu Buhari da Samuel Ortom Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

'Yan siyasa iri biyu ne - Garba Shehu

Malam Shehu ya ce akwai ‘yan siyasa iri biyu a Najeriya a yau. Na farko su ne masu neman mafita, na biyu su ne masu neman uzuri, su na daura laifinsu ga wasu.

Kara karanta wannan

Kotu ta yankewa wasu masu walder 4 daurin shekaru 7 a kurkuku saboda satar N15m

Hadimin yake cewa Buhari ya samu babu komai a baitul-mali, amma ya yi ta kokarin karbo kudin da aka sace, ya gano asusun da ake yin gaba da kudin gwamnati.

“Buhari Shugaban kasa ne da bai gagara biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya ba, ya ma zargi jihohin da suka gaza sauke nauyinsu da cewa an yi abin kunya.”
“Saboda a magance wannan matsala, a lokuta da-dama ya ba jihohi aron N1.682tr, ko yaushe sai an raba wadannan kudin da jihar Benuwai ta Samuel Ortom.
“Yanzu haka shi ne gwamnan da ya fi kowa tarihin daukar mafi tsawon lokaci bai biya albashi da fansho ba, bai da wani dalilin da zai rika sukar Buhari.”

A maida hankali kan albashi

Kwanakin baya haka aka ji wata kungiyar matasan Tiv ta yi kira ga Gwamna Samuel Ortom da ya maida hankali kan aikin gabansa a maimakon sukar shugaban kasa.

Shugaban kungiyar, Hon. Mike Msuaan, ya fadi hakan ne yayin da yake martani ga Ortom bayan ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari a hira da aka yi da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel