Da dumi-dumi: Tsagin shekarau ya sake yin nasara kan tsagin Ganduje a kotu

Da dumi-dumi: Tsagin shekarau ya sake yin nasara kan tsagin Ganduje a kotu

  • Wata kotu a babban birnin tarayya Abuja ta bayyana kin amincewa da bukatar 'yan tsagin Ganduje kan batun soke zaben taron gangamin APC
  • An kai batun kotu ne yayin da 'yan tsagin Ganduje suka ce basu amince da hukuncin kotu na tabbatar da ingancin zaben ba
  • Siyasar jam'iyyar APC a jihar Kano ta kara rincabewa tun bayan da aka yi taron gangamin APC na jihohi

Abuja - Wata babbar kotun birnin tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar da wasu ‘yan jam’iyyar APC na jihar Kano da ke biyayya ga gwamna Ganduje suka nema na yin watsi da hukuncin da ya tabbatar da zabukan jam’iyyar a taron gangaminta da aka yi.

Kotun da ke zama a karkashin Mai shari’a Hamza Muazu ta kuma ki amincewa da batun da aka shigar na dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an yanke hukuncin daukaka kara a kotun daukaka kara, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Matar aure ta tsere da saurayinta ta bar mijinta da suka shafe shekaru 3 tare

Ganduje ya fadi a kotui
Da dumi-dumi: Tsagin shekarau ya sake yin nasara kan tsagin Ganduje a kotu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kotun dai a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2021, ta tabbatar da zaben unguwanni da na kananan hukumomi da ake kyautata zaton 'yan tsagin Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Jibril Barau (Kano ta Arewa) ne suka lashe zaben da adadinsu ya kai 17,908.

Kotun dai ta ki amincewa da matakin farko na 'yan tsagin Gwamna Ganduje da ke kalubalantar sakamakon.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotu ta tabbatar da tsagin Shekarau matsayin sahihan shugabannin APC a Kano

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin Mai Sharia Hamza Muazu ta tabbatar da tsagin Shekarau ta gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar APC a Kano.

Yayin Shari'a ranar Juma'a, Alkalin ya yi watsi da karar tsagin Ganduje kuma ya ci su tarar milyan daya kan batawa kotu lokaci, rahoton DailyNigerian.

Kotu ta tabbatar da cewa zaben da tsagin Shekarau tayi shine daidai kuma shugabanninsu ne shugabannin APC a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka

A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya magantu kan bukatarsa na sasantawa da abokin hamayyarsa, tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso da tsagin APC karkashin shugabancin Sanata Ibrahim Shekarau.

A sakon sabuwar shekara, wanda kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba yasa hannu a ranar Juma'a, Ganduje ya ce zai sadaukar da sabuwar shekarar wurin tabbatar da sabon tsarin zaman lafiya da sasanci tsakanin masu ruwa da tsakin jam'iyyun siyasa a jihar da kasar baki daya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, duk da gwamnan bai kira sunayen 'yan siyasan ba, takardar ta jaddada bukatar shugabannin kungiyoyin siyasa na jihar da su hada kai domin kawo sabon tsari a siyasar jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel