Sam bai dace ba: Martanin yan Najeriya kan dokar dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano

Sam bai dace ba: Martanin yan Najeriya kan dokar dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano

  • A yau Litinin, 24 ga watan Janairu ne gwamnatin Kano ta sanar da dakatar da lasisin makarantun kudi a jihar
  • Matakin na zuwa ne bayan garkuwa da halaka Hanifa Abubakar, yarinya mai shekaru 5 da mamallakin wata makarantar kudi ya yi
  • Sai dai wannan mataki bai gamsar da yan Najeriya da dama ba inda suka soke shi tare da kalubalantarsa

Kano - Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakunansu a kan matakin da gwamnatin Kano karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta dauka na dakatar da lasisin makarantu masu zaman kansu a jihar.

Gwamnatin Kano dai ta ce za ta kafa wani kwamiti na musamman wanda zai tantance makarantu kuma za ta fitar da wasu matakai da za a yi amfani da su wurin tantance makarantun kudi a jihar.

Sai dai wannan mataki bai gamsar da mutane da dama ba inda suke ganin hakan zai zama tauye malaman makarantun wadanda da wannan koyarwar ne suka dogara.

Har ila yau wasu na ganin hakan zai haifar da rudani da kuma koma baya a harkar ilimi a jihar domin zai kawo tsaiko ga karatun daliban.

Sam bai dace ba: Martanin yan Najeriya kan dokar dakatar da lasisin makarantun kudi
Sam bai dace ba: Martanin yan Najeriya kan dokar dakatar da lasisin makarantun kudi Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin jama'a

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin da mabiyanta na Facebook suka yi.

Aleeyu Amiin ya ce:

"To gsky Wannan mataki bai dace ba Duba ga malamai xasu shiga wani hali Sannan karatun yara xai gamu da cikas anawa ra ayi tsaurara matakai ya dace kawai tareda fatan ayiwa Hanifa Adalci."

Mustapha Yakub Adam ya yi martani:

"Subhanallah. To amma malaman makaran tun kudi su kuma ya xa ai dasu kenan. Ko suma suna karbar salary ko da kuwa basa Aiki."

Musa Umar ya ce:

"Gaskiya na shiga rudani.. Mu da muke koyarwa a private schools kuma muyi yaya? Muna da kannenmu da muke kula da su.
"Wasunmu suna da aure da yara kuma sun dogara ne da dan abun da suke samu daga wadannan makarantu. Ta wannan albashi da muke karba a wuraren aikinmu ne muke biyan kudin hayar gida, tura yaranmu makaranta kuma daga makarantar ne muke samun abun biyan bukatunmu na yau da kullun.
"Ina rokon gwamnatin jihar da ta sake duba wannan hukunci."

Ali Garba ya ce:

"Cewa akai ansoke lasisi bacewa akai andakatar da karatunba yakamata mutane suringa fahintar magana."

Wata sabuwa: Ganduje ya dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano

A baya mun kawo cewa Gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya dakatar da dukkan lasisin makarantun kudi da ke fadin jihar, har sai zuwa lokacin da aka tantance su.

Sanusi Sa'id Kiru, kwamishinan ilimi na jihar Kano ne ya tabbatar da hakan lkacin da ya ke ganawa da manema labarai.

Wannan al'amarin na zuwa ne bayan 'yan sanda sun gurfanar da mamallakin makarantar Noble Kids a gaban kotu, Abdulmalik Tanko, wanda ya amsa kashe Hanifa Abubakar, yarinya mai shekaru biyar, BBC Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel