Nasara: Dakarun sojin Najeriya sun sheƙe ƴan ta'adda 49, 863 sun miƙa wuya, DHQ

Nasara: Dakarun sojin Najeriya sun sheƙe ƴan ta'adda 49, 863 sun miƙa wuya, DHQ

  • Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta sanar da sheka 'yan ta'adda 49 da dakarun sojin kasar nan suka yi a cikin makonni 2 kacal
  • Baya ga hakan, 'yan ta'adda a garuruwan Banki, Bama, Dikwa, Gwoza da Gamboru da ke Borno har 863 sun mika wuya ga dakarun
  • An samu miyagun makamai masu yawa, shanun sata, motocin yaki hudu da sauran su daga 'yan ta'addan

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaron kasa ta ce ta halaka 'yan ta'addan 49 a karkashin ayyukan sojojin ta yayin da 'yan ta'addan 863 suka mika makaman su a makonni biyu da suka gabata.

Daraktan yada labarai, Bernard Onyeuko, ya sanar da hakan yayin bayar da bayani kan ayyukan sojojin a ranar Alhamis a Abuja, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta, sun halaka 4, wasu sun jigata

Onyeuko ya ce sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun halaka 'yan ta'adda 37, sun cafke 17 tare da samo miyagun makamai 117.

Nasara: Dakarun sojin Najeriya sun sheƙe ƴan ta'adda 49, 863 sun miƙa wuya, DHQ
Nasara: Dakarun sojin Najeriya sun sheƙe ƴan ta'adda 49, 863 sun miƙa wuya, DHQ. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya kara da cewa, sun kama motocin yaki hudu na 'yan ta'addan yayin da suka ceto mutum 16 da aka yi garkuwa da su duk a cikin makonni biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Onyeuku ya ce 'yan ta'addan 863 tare da iyalan su da suka kunshi maza manya 136, mata manya 251 da kananan yara 486 sun mika wuya ga dakarun sojin.

Ya ce sun mika kansu a wurare daban-daban da suka hada da Banki, Bama, Dikwa, Gwoza da Gamboru da ke Borno.

"Yan ta'addan da suka mika wuya an karbe su kuma an dauka bayanansu tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar matakin gaba.
"A hakan, dakarun sojin saman sun rikita 'yan ta'addan a wuraren da suka mamaye kamar kauyen Arina Chiki da ma yankin tafkin Chadi a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sojoji sun gasa wa 'yan ISWAP ayya a hannu yayin da suka kai hari a Biu

"Wannan ya yi sanadain halaka wasu daga cikin 'yan ta'addan yayin da wasu suka tsere da miyagun raunika.
"An samu wannan nasarar ne a ranar 14 ga watan Janairu yayin da aka samu bayanan sirri kuma aka aike sojin sama yankin da 'yan ta'addan ke taron su. Sojin saman sun yi wa 'yan ta'addan ruwan wuta ta sama," yace.

A wani aiki na sojojin, Onyeuko ya ce dakarun sun halaka 'yan ta'adda 12 tare da cafke masu basu bayanai 15. Ya kara da cewa an kwace makamai masu hadari tare da shanun sata 114.

Premium Times ta ruwaito cewa, ya ce dakarun sun kwato miyagun bindigogi da kuma babura hudu sai suka ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su.

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe ƴan sanda 3 da ƴan sa kai 2

A wani labari na daban, rundunar ƴan sandan jihar Neja ta tabbatar da kisan uku daga cikin jami'an ta da ƴan sa kai biyu mazauna yankin yayin da ƴan bindiga su ka yi kwantan ɓauna a Kwanan Dutse, karamar hukumar Mariga da ke jihar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas

Kwamishinan ƴan sanda, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da hakan ne a ranar Talata yayin tattaunawar waya da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Minna.

Kuryas ya ce al'amarin ya auku ne a ranar Litinin misalin karfe 4:00 na yamma yayin da Jami'an Tsaron Hadin gwuiwa, wanda ya kunshi ƴan sanda da ƴan sa kai yayin da suka fita sintiri a yankin, Premium Times ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel