Da Dumi-Dumi: Kungiyar kwadugo NLC ta dakatar da gagarumar zanga-zangar da ta shirya a faɗin Najeriya

Da Dumi-Dumi: Kungiyar kwadugo NLC ta dakatar da gagarumar zanga-zangar da ta shirya a faɗin Najeriya

  • Ƙungiyar kwadugo ta ƙasa NLC ta janye shirinta na zanga-zanga a faɗin Najeriya kan cire tallafin man Fetur
  • Shugaban NLC na ƙasa, Ayuba Waba, ya ce kasancewar gwamnati ta dakatar da shirin cire tallafin, shiyasa suka ɗauki wannan matakin
  • Yace NLC ta yanke wannan hukuncin ne bayan taron yan majalisar shugabanni, wanda ya gudana yau Talata

Abuja - Ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) ta dakatar da gagarumar zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a ranar 27 ga watan Janairu, 2021.

Vanguard ta ruwaito cewa NLC ta shirya yin zanga-zangan ne domin nuna adawa da shirin gwamnatin tarayya na zare tallafin man Fetur.

Shugaban ƙungiyar NLC, Ayuba Waba, shi ne ya bayyana haka yayin da yake zanta wa da manema labarai a Labour House, Abuja.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Rikici ya barke a Legas, gwamnati ta dakatar kungiyar sufuri ta NURTW

Kungiyar kwadugo NLC
Da Dumi-Dumi: Kungiyar kwadugo NLC ta dakatar da gagarumar zanga-zangar da ta shirya a faɗin Najeriya Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne a taron zaɓaɓɓun shugabanninta wanda ya gudana ranar Talata da safe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Waba ya ƙara da cewa sun janye zanga-zangan ne, kasancewar gwamnatin tarayya ta dakatar da shirinta na zare tallafin man fetur.

Wane mataki NLC zata ɗauka na gaba?

A cewar shugaban NLC, mambobin ƙungiyar da suka tattaru domin gudanar da zanga-zangan zasu sallami kowa biyo bayan matakin janye lamarin.

The Cable ta rahoto yace:

"Bayan matakin da gwamnati ta ɗauka, majalisar shugabannin kungiyar NLC sun gana ta hanyar amfani da fasahar zamani ranar Talata, domin nazari kan matakin gwamnati."
"Bayan doguwar muhawara yayin ganawar NEC, mun amince da janye zanga-zangan da muka shirya gudanarwa ranar 27 ga watan Janairu, da kuma ta ƙasa a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2022."

A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar PDP ta dakatar da Surukin gwamnanta da wasu jiga-jigai uku, zasu koma APC

Kara karanta wannan

Fitaccen ɗan Kasuwa dake kasar waje ya sanar da shiga tseren maye gurbin shugaba Buhari a 2023

Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Benuwai ta dakatar da manyan jiga- jiganta guda huɗu, ciki har da surukin gwamnan jihar, Samuel Ortom.

Rahotanni sun bayyana cewa APC na ta shirye-shiryen karɓan wasu manyan PDP a jihar, cikin su har da waɗan da aka dakatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262