Shugaban yan Najeriya a kasar waje ya ayyyana kudirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023

Shugaban yan Najeriya a kasar waje ya ayyyana kudirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Shugaban yan Najeriya dake ƙasar Japan, Chief Nnaji, ya ayyana kudirin maye kujerar shugaba Buhari a babban zaɓen 2023
  • Nnaji yace Najeriya na bukatar mutanen da suka fita waje suka kware, domin su gwada basirar da Allah ya ba su wajen haɗa kan Najeriya
  • Yace ya amince ya nemi shugaban ƙasa ne domin gyara kasar ta shiga jerin kasashen da za'ayi gogayya da su a duniya

Shugaban ƙungiyar yan Najeriya dake zaune a ƙasar waje, Chief Kennedy Fintan Nnaji, ya bayyana shiga tseren kujerar shugaban ƙasa a babban zaben 2023, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Chief Nnaji wanda ya kwashe zango biyu a matsayin mai taimaka wa kungiyar marubuta wasanni (SWAN) reshen jihar Legas, ya sanar da shirin takararsa a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Kano: Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa Abubakar, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma

Chief Nnaji
Shugaban yan Najeriya a kasar waje ya ayyyana kudirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Fitaccen ɗan kasuwan ɗan kimanin shekara 53 a duniya ya ce ya ɗauki matakin neman maye gurbin shugaba Buhari a 2023 ne saboda akwai bukatar ya kawo kwarewarsa ta kasar waje zuwa Najeriya.

Guardian ta rahoto Nnaji yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An samu sabani tsakanin yan Najeriya, wanda mutane masu son kai suka ƙara rura wutar sabanin. Babu ƙasar da za ta samu cigaba matukar ba tare da haɗin kan yan ƙasa ba."
"Wajibi yan Najeriya su haɗa kan su, domin ƙasar ta samu ɗaukaka. Ina da kyakkyawan nufin na dawo na samar da yanayi mai kyau tsakanin yan Najeriya."

A wace jam'iyya zai nemi takarar shugaban ƙasa?

Dangane da jam'iyyar siyasa wacce zai shiga takarar shugabancin Najeriya, ɗan kasuwan yace ba da jimawa ba zai sanar kowa ya sani.

A cewarsa, lokaci ya yi da yan Najeriya za su jaraba kwarewar mazauna ƙasashen waje a manyan muƙaman siyasa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan harin rashin imani jihar Neja, sun halaka dandazon mutane

Yace ba wai kwarewarsa kaɗai zai kawo Najeriya ba, xai haɗa kan yan kasa baki ɗaya kamar yadda ya dunƙule yan Najeriya dake zaune a Japan.

"Manufa ta shi ne na gyara Najeriya ta zama kasar da za ta yi gogayya da sauran ƙasashen duniya."

A wani labarin na daban kuma Kotun tarayya dake Abuja ta bada umarnin kamo tsohuwar ministan Man fetur ko ina aka ganta

Alkalin kotun, mai Shari'a Bolaji Olajuwon, shi ya bada umarnin ranar Litinin, biyo bayan bukatar da lauyan hukumar yaƙi da cin hanci, (EFCC), Farouq Abdullah, ya gabatar.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta na tuhumar Diezani da sama da faɗi da dukiyar ƙasa, amma ta yi biris, ta ɓoye a Burtaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel