Daga karshe: Gwamnatin Kwara ta amince mata musulmai suke sanya hijabi a makarantu

Daga karshe: Gwamnatin Kwara ta amince mata musulmai suke sanya hijabi a makarantu

  • Bayan da aka samu rikice-rikice kan lamuran da suka shafi addini a jihar Kwara, gwamnati ta fitar da mafita
  • Gwamnati ta amince da mata musulmai su sanya hijabi a makarantun gwamnati na fadin jihar ta Kwara
  • An kuma bukaci makarantun gwamnati da su dauki umarnin, sannan su tabbatar da fara bin dokar da aka sa

Jihar Kwara - Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kwara ta ce ‘yan mata musulmi da ke son shiga makarantun gwamnati a yanzu suna da ‘yancin sanya Hijabi a makaranta.

Kwamishiniyar ilimi ta jihar Hajia Sa’adatu Modibbo Kawu ce ta bayyana hakan a lokacin wani taron zaman lafiya da masu ruwa da tsaki na musulmi da kirista a garin Ijagbo dake karamar hukumar Oyun ta jihar.

Gwamnatin Kwara ta samo mafita ga rikicin sanya hijabi
Daga karshe: Gwamnatin Kwara ta amince mata musulmai suke sanya hijabi a makarantu | Hoto: leadersip.ng
Asali: Facebook

A cewar kwamishinar:

Kara karanta wannan

Kada dai a samu hanyar tatsar masu makarantun kudi: PDP ta gargadi Ganduje kan batun lasisin makarantun kudi

“Bayanin manufofin gwamnatin jihar Kwara na ba wa ‘yan mata musulmai damar sanya hijabi a duk makarantun gwamnati, ciki har da wadanda ake ba tallafin karatu. Wannan ya yi daidai da hukunce-hukuncen shari’a na kotunan shari’a da kuma kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.”

Don haka ta yi kira ga shugabannin Musulmi da Kirista da su bari a samu zaman lafiya a jihar.

Hajiya Modibbo-Kawu ta kuma umurci shugaban makarantar Oyun Baptist High School, Ijagbo da ta gaggauta aiwatar da sanarwar manufofin gwamnati kan sanya hijabi da aka amince da su a makarantun gwamnati.

Ta yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana kokarin kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar zai fuskanci fushin doka, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Taron ya samu halartar sakatariyar dindindin, Misis Mary Adeosun; shugaban hukumar aikin koyarwa, Alhaji Taoheed Bello da shugabannin hukumar kula da ayyukan koyarwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kwara ta haramta bara a jihar, ta yi yarjejeniyar da al'ummar Hausawar Ilori

Hakazalika, shugaban kungiyar shugabannin makarantun sakandire ta Najeriya (ANCOPSS), Alhaji Toyin Abdullahi da shugaban kungiyar malamai ta Najeriya (NUT), Alh Umar Abdullahi duk sun hallara

A bangaren taron an samu halartar shugabannin addinai na kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen Ijagbo, Rabaran Samuel Ajayi da shugaban masu ruwa da tsaki na musulmin Offa/Oyun, Alh Abubakar AbdulWasiu da dai sauransu.

Hana dalibai sanya hijabi a Boko: Gwamnan jihar Kwara ya kulle makarantu 10

A wani labarin a can baya, gwamnatin jihar Kwara a ranar Juma'a ta bada umurnin kulle wasu makarantu mallakin coci a Ilori har sai an kammala tattaunawa kan lamarin hana dalibai sanya hijabi a makarantun.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sakatariyar din-din-din na ma'aikatar ilimin jihar, Kemi Adeosun, ta saki jawabin cewa makarantun da hakan ya shafa sun hada da Cherubim and Seraphim (C&S) College, Sabo Okea d St.

Anthony College, Offa Road. Sauran sune ECWA School, Oja Iya, Surulere Baptist Secondary School da Bishop Smith Secondary School, Agba Dam.

Kara karanta wannan

Kisan gillar Hanifa: Gwamna Ganduje ya magantu, ya bayyana matakin da za a dauka

Asali: Legit.ng

Online view pixel