Hana dalibai sanya hijabi a Boko: Gwamnan jihar Kwara ya kulle makarantu 10

Hana dalibai sanya hijabi a Boko: Gwamnan jihar Kwara ya kulle makarantu 10

Gwamnatin jihar Kwara a ranar Juma'a ta bada umurnin kulle wasu makarantu mallakin coci a Ilori har sai an kammala tattaunawa kan lamarin hana dalibai sanya hijabi a makarantun.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sakatariyar din-din-din na ma'aikatar ilimin jihar, Kemi Adeosun, ta saki jawabin cewa makarantun da hakan ya shafa sun hada da Cherubim and Seraphim (C&S) College, Sabo Okea d St. Anthony College, Offa Road.

Sauran sune ECWA School, Oja Iya, Surulere Baptist Secondary School da Bishop Smith Secondary School, Agba Dam.

Hakazalika akwai CAC Secondary School, Asa Dam, St. Barnabas Secondary School, Sabo Oke, St. John School, Maraba, St. Williams Secondary School, Taiwo Isale da St. James Secondary School, Maraba.

Hana dalibai sanya hijabi a Boko: Gwamnan jihar Kwara ya kulle makarantu 10
Hana dalibai sanya hijabi a Boko: Gwamnan jihar Kwara ya kulle makarantu 10
Source: UGC

Tace: "An kulle makarantun bayan kwamitin da gwamnati ta kafa wanda ya kunshi Musulmai da Kirista ta zauna a ranar Juma'a don tattaunawa kan lamarin."

"Gwamnati na kira ga al'ummar jihar su kwantar da hankulansu kuma su guji kalamai da ka iya raba kan al'umma."

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa wasu makarantun mission a Kwara sun haramtawa dalibai Musulmai sanya hijabi.

Lamarin ya yi kamari ne lokacin da aka fara koran dalibai mata masu hijabi daga cikin aji.

Source: Legit.ng

Online view pixel