Ango ya danƙara wa amarya saki a liyafar bikinsu kan waƙar da ta zaɓa a saka mata

Ango ya danƙara wa amarya saki a liyafar bikinsu kan waƙar da ta zaɓa a saka mata

  • Ango ya dankara wa amarya saki ana tsaka da liyafar bikin su a birnin Baghdad saboda wakar da ta zaba a saka mata
  • Kamar yadda wani sashin wakar ke cewa, ni ce mai rinjaye kuma dole zan mulke ka, ka kuma bi umarni na matukar muna tare
  • Amarya ta tashi ta dinga rawa tare da girgijewa, lamarin da ya fusata ango da danginsa har ta kai ga an yi kaca-kace da 'yan uwan amarya

Wasu ango da amarya sun kafa sabon tarihi na yin aure mafi gajarta a duniya. Sun rabu ne a yayin da ake liyafar bikin su saboda wakar da amaryar ta zaba.

A take kuwa angon ya dankara wa amaryar saki bayan rikicin da wakar ta janyo yayin da ake tsaka da shagalin bikin a Baghdad.

Kamar yadda aka tattaro, matar ta bukaci a saka mata wata wakar kasar Syria ne mai suna Mesaytara wacce Lamis Kan ya rera.

Kara karanta wannan

Dan Allah ku taya ni da addu’ar samun lafiya, Olisa Metuh ya roki ‘yan Najeriya

Ango ya danƙara wa amarya saki a liyafar bikinsu kan waƙar da ta zaɓa a saka mata
Ango ya danƙara wa amarya saki a liyafar bikinsu kan waƙar da ta zaɓa a saka mata. Hoto daga BBC.com
Asali: UGC

Wakar ta fara da cewa:

"Ni ce mai rinjaye; za ka mulku a karkashin tsauraran dokoki na, zan haukata ka idan ka kalla wasu 'yan mata a titi.
"Tabbas, ni ce mai rinjaye, kai ne sukari na. Idan har ina tare da kai, dole ne ka yi aiki da umarni na."

An gano cewa, amaryar ta tashi ta dinga rawa tare da girgijewa yayin da aka saka mata wakar, amma hakan bai yi wa 'yan uwan ango dadi ba, lamarin da ya tada tarzoma tsakanin iyalan biyu.

Ba wannan ba ne karo na farko da wannan wakar ta fara kashe aure ba, wakar ta kashe wani aure a kasar Jordan a shekarar da ta gabata, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Bidiyo da hotunan 'yar Najeriya mai shekaru 61 da ta yi aure a karon farko a Jamus

Kara karanta wannan

Babbar magan: Gwamna ya sanya hannu ya doka mai tsauri ta hana kiwo a fili

A wani labari na daban, wata ‘yar Najeriya mai shekaru 61, mai suna Lizzy Taiwo, ta fita daga kasuwar ‘yan mata inda ta zama matar aure cikin kwanakin nan ga babban abokinta Colins.

Instablog9ja ta wallafa hotuna da bidiyoyin bikin wadanda aka ga amaryar da bata taba haihuwa ko kuma aure ba a rayuwarta.

An yi auren tsakanin Lizzy da Collins ranar Asabar, 15 ga watan Janairu a can cikin kasar Jamus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel