Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello

Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da masoyiyarsa, Nerita Ezenwa sun halarci taron haska fim din tarihin Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi a ranar Lahadi
  • Mutane 200 aka zaba don halartar taron haska fim din mai suna ‘Yahaya the White Lion’ ma’ana, Yahaya farin Zaki, wanda aka yi a Transcorp Hilton a Abuja
  • A fim din, Ali Nuhu ne ya taka rawar Bello yayin da Roseannr Chikwendu ta taka rawar matar sa, Rashidat Bello, kuma Tunde Laoye ya bayar da umarnin shirin

Abuja - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da matarsa, Nerita Ezenwa, masoyiyar sa, a ranar Lahadi sun halarci taron haska shirin fim din tarihin rayuwar Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi.

Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello
Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An zabi mutane 200 don halartar taron haska fim din mai suna ‘Yahaya the White Lion’ ma’ana ‘Yahaya farin Zaki’ a Transcorp Hilton da ke Abuja, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta bada umarnin kamo tsohuwar Minista ko ina aka ganta

Jarumi Ali Nuhu ne ya taka rawar Bello yayin da Roseanne Chikwendu ta taka rawar Rashidat Bello, matar gwamnan.

Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello
Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shirin wanda Tunde Laoye ya bayar da umarni, ya haska jarumai kamar Gbenga Adeyinka da Aishat Lawal.

Furodusan fim din, Seun Oloketuyi ya shirya fim din don duba akan rayuwar gwamnan.

Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello
Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello. Hot daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda yace:

“Ana ta fadin abubuwa dangane da mutumin nan, Yahaya Bello, amma har yanzu akwai abubuwa da dama da ba a sani ba dangane da shi.

Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello
Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello. Hot daga thecable.ng
Asali: UGC

“An shirya shirin ne don dubi a kan rayuwar gwamnan, yadda ya girma kuma ya tasa, siyasar sa da kuma burin sa na gaba. Gaba daya tarihin rayuwar gwamnan aka bayyana a fim din.”

TheCable ta ruwaito cewa, auren Fani-Kayode da Precious Chikwendu ya rabu ne a shekarar 2020 bayan ta zarge shi da dukan ta yayin da ministan ya zarge ta da rashin kamun kai.

Kara karanta wannan

EFCC ta na binciken mutum 5 a cikin masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC

Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello
Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Tsohon ministan ya yi aure-aure hudu. Ya yi auren sa na farko da Saratu Attah a 1987.

Sun rabu bayan shekaru 3 da aure lokacin sun haifa diya mace, Oluwafolake. A 1991, Fani-Kayode ya auri Yemisi Adeniji amma suka rabu a 1995.

Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello
Hotunan Fani-Kayode da zukekiyar masoyiyarsa a wurin haska fim din Yahaya Bello. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya yi auren sa na uku da Gina Hall a 1997. Bayan sun haifi diyarsu Oluwaremilekun sai ya auri Chikwendu a 2014 wacce ba su dade da rabuwa ba.

Hotunan Fani-Kayode da wasu mutum 3 da EFCC ta sake gurfanarwa kan damfarar N1.5bn

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, a ranar Litinin, 24 ga watan Janairun 2022 ta sake gurfanar da tsohuwar ministar kudi, Nnenadi Esther Usman da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode kan damfarar wasu makuden kudade.

A tare da su akwai Yusuf Danjuma, tsohon shugaban ALGON da kuma wani kamfani mai suna Joint-Trust Dimensions Nigeria Limited.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mutane sun shiga daji sun kwato Sarkin su da yan bindiga suka sace a Filato

Ana zargin su da laifuka 17 da suka hada da hadin kai wurin yin cuta da kuma adana kudi ba bisa ka'ida ba da suka kai naira biliyan daya da rabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel