Katsinawa sun fada tashin hankali bayan an janye sojoji daga yankunan jihar

Katsinawa sun fada tashin hankali bayan an janye sojoji daga yankunan jihar

  • Hankalin jama'a mazauna yankunan karamar hukumar Safana ta jihar Katsina ya tashi kan janye sojoji da aka yi daga yankunan a ranar Litinin
  • Wani mazaunin yankin mai suna Sani Safana ya tabbatar da cewa, da yammacin ranar Litinin sun hango wani dan bindiga ya fara zuwa kewaye, sa'o'i kadan bayan tafiyar sojojin
  • Sai dai dan majalisa mai wakiltar mazabar, Abduljalalu Haruna, ya tabbatar da cewa sojojin za su koma saboda hankalin jama'a ya tashi ganin cewa ba su da mataimaki sai Allah

Safana, Katsina - Mazauna garin Runka da wasu yankuna na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina sun bayyana tsoron su kan makomar su bayan kwashe sojojin yankin da aka yi a ranar Litinin.

Sojoji da ke aikin hadin guiwa na tsaro suna da sansani a Runka, gari na biyu mafi girma a karamar hukumar Safana ta jihar, har zuwa jiya Litinin da aka janye su, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa

Mazauna yankin sun ce 'yan ta'adda sun sanya wa Runka ido ganin irin tsaro da suke fuskanta, hakan ne kuwa ya kange su daga farmakin miyagun.

Katsinawa sun fada tashin hankali bayan an janye sojoji daga yankunan jihar
Katsinawa sun fada tashin hankali bayan an janye sojoji daga yankunan jihar. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Safana ta na daya daga cikin kananan hukumomi 13 na jihar Katsina da ke fama da matsalar tsaro. A shekarar da ta gabata, an datse kafofin sadarwa a yankin daga cikin matakan yaki da miyagu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abduljalalu Haruna, dan majalisa mai wakiltar mazabar Safana a majalisar jihar ya yi kira kan a janye wannan batun kwashe sojoji daga yankin.

Haruna ya ce yankin zai zama wuri mafi sauki da 'yan ta'addan za su dinga kai farmaki idan babu jami'an tsaro.

A yayin zantawa da Premium Times, dan majalisar ya ce ya shiga damuwa kan yadda mazabar sa za ta kasance.

"A yanzu haka da na ke muku magana, ina kiran wadanda ya dace domin a cire tsoro daga zukatan mutane kuma a san yadda za a yi jami'an tsaro su dawo. Na yi magana da cibiyoyin tsaron da suka dace, sun ce za a mayar da su yankunan," Haruna yace.

Kara karanta wannan

Samun man fetur ya yi wahala, jama'a sun koka, sun ce za su fara zanga-zanga

Sani Safana, wani shugaban matasa ya ce sun hango wani da ake zargin dan bindiga ne da yammacin Litinin a filin kwallo da ke Runka, sa'o'i kadan bayan sojojin sun tafi.

Safana ya ce yankunan su suna cikin fargaba, wuraren sun hada da Runka, Gora, 'Yalilo, Maikada da wasu yankunan yammacin garin Safana.

Amma kuma da aka tuntubi Muhammad Katsina, mai bada shawara kan tsaro ga Gwamna Aminu Masari, ya ce bai san da batun janye sojoji daga yankin ba.

"Zan fara ji daga bakin hukumomin tsaro saboda ta yuwu wani sabon tsarin tsaro ne," yace.

Nasara: Soji sun bankado farmakin 'yan ta'adda, sun ceto dan siyasa da iyalinsa a Zamfara

A wani labari na daban, sojoji tare da taimakon 'yan sa kai a daren Asabar sun ceto wani dan siyasa da iyalansa bayan musayar wuta da suka yi da 'yan ta'addan inda aka kashe 'yan ta'adda masu yawa.

Kara karanta wannan

Zamfara APC: Rikici ya dauka sabon salo, ana amfani da 'yan daba wurin kai farmaki

Majiyoyi daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara, sun tabbatar wa da Premium Times cewa, an sace dan siyasa Aminu Adamu a gidan sa da ke kwatas din Mareri da ke birnin.

Adamu wanda aka fi sani da Papa, shi ne manajan daraktan hukumar sufuri ta jihar Zamfara kuma makusancin Gwamna Bello Matawalle.

Asali: Legit.ng

Online view pixel