Kisan Hanifa: An samu fusatattun matasan da suka bi dare, suka cinna wuta a makaranta

Kisan Hanifa: An samu fusatattun matasan da suka bi dare, suka cinna wuta a makaranta

  • Wasu mutane sun je sun banka wuta a makarantar nan ta Noble Kids School da ke jihar Kano dazu
  • Rahotanni sun bayyana cewa an sa wuta a wannan makaranta da ke unguwar Kawaji ne da tsakar dare
  • Kona makarantar ba ta rasa alaka da kisan wata karamar yarinya Hanifa da mai makarantar ya yi

Kano - Rahotanni su na zuwa cewa wasu mutane sun banka wuta ga makarantar Noble Kids, wanda makashin Hanifa Abubakar ya mallaka.

Daily Nigerian ta bayyana cewa wasu mutane sun je wannan makaranta da ke kan titin Warshu Hospital a unguwar Kawaji, sun sa mata wuta.

Ana zargin dalilin yin hakan shi ne saboda mamallakin makarantar, Abdulmalik Tanko ya sace wata daliba mai shekara 5 a Duniya, ya kashe ta.

Kara karanta wannan

Labari ne mai ban tsoro - Dattawan arewa sun yi Allah wadai da kisan Hanifa

Malam Abdulmalik Tanko ya kashe wannan Baiwar Allah da guba, sannan ya daddatsa ta, duk da ya karbi kudin fansa daga hannun ‘yanuwanta.

A tsakar daren yau Litinin, 24 ga watan Junairu 2022, sai kawai aka ji labarin makarantar Noble Kids School da ke garin Kano ta na ta ci da wuta.

Kisan Hanifa
Makarantar su Hanifa Hoto: @ahmed.princegandujiyya.9
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har zuwa lokacin da jaridar ta samu rahoto a cikin dare, ba a iya kashe wannan wuta ba. An samu bidiyon makarantar ta na ci da wuta a Instagram.

Hakan na zuwa ne duk da gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin ayi maza a garkame wannan makarantar saboda gudun irin hakan ta faru.

Halin da ake ciki

Yanzu haka mai wannan makaranta yana hannun jami’an tsaro, kuma ya amsa laifinsa da bakinsa.

Mutane su na ta kira ga hukuma ta dauki matakin da ya dace, ta hukunta wannan malami da ya kashe yarinyar da ba ta ji ba, ba ta gani ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bada umurnin rufe makarantar da aka kashe Hanifa Abubakar

Kawo yanzu jama’a su na ta yin Allah-wadai da abin da ya faru, sannan kuma an yi tir da yadda wasu suka dauki doka a hannu, suka cinna wuta.

Kafin mutane su sa wuta a makarantar, an ji cewa Ministan sadarwa na kasa, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya je ya yi wa iyayen Hanifa ta’aziyya.

Shekarau ya yi magana

Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya yi magana a game da kisan Hanifa Abubakar.

Malam Ibrahim Shekarau ya sha alwashin daukan mataki domin ganin an hukunta Abdulmalik Tanko, wanda ya kashe wannan 'yar karamar yarinyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel