Wata sabuwa: Ganduje ya dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano

Wata sabuwa: Ganduje ya dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke fadin jihar
  • A cewar kwamishinan ilimi na jihar, gwamnati za ta kafa kwamiti domin tantance makarantun kudin
  • Wannan al'amarin ya na zuwa ne bayan garkuwa da halaka yarinya mai shekaru 5 da mamallakin wata makarantar kudi ya yi

Kano - Gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya dakatar da dukkan lasisin makarantun kudi da ke fadin jihar, har sai zuwa lokacin da aka tantance su.

Sanusi Sa'id Kiru, kwamishinan ilimi na jihar Kano ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya ke ganawa da manema labarai.

Wata sabuwa: Ganduje ya dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano
Wata sabuwa: Ganduje ya dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Wannan al'amarin na zuwa ne bayan 'yan sanda sun gurfanar da mamallakin makarantar Noble Kids a gaban kotu, Abdulmalik Tanko, wanda ya amsa kashe Hanifa Abubakar, yarinya mai shekaru biyar, BBC Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sam bai dace ba: Martanin yan Najeriya kan dokar dakatar da lasisin makarantun kudi a Kano

A cewarsa, za a kafa wani kwamiti na musamman wanda zai tantance makarantu kuma za ta fitar da wasu matakai da za a yi amfani da su wurin tantance makarantun kudi a jihar.

Hakazalika, ya ce dukkan makarantun masu zaman kansu da ba su cika sharuddan da za a gindaya musu ba, sun tafi kenan, ma'ana ba za a bude su ba.

Aiki ga mai yin ka: Sanata Shekarau ya magantu kan kisan Hanifa, ya sha muhimmin alwashi

A wani labari na daban, Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya sha alwashin daukar mataki da kan sa kan kisan gillar da aka yi wa Hanifa, yarinyar da aka yi garkuwa da ita kuma daga bisani aka kashe a Kano.

Kara karanta wannan

Neman adalci: Makashin Hanifa ya bayyana a kotu, an dage shari'a zuwa wasu kwanaki

Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar da Hanifa ke zuwa, ya tabbatar da kashe yarinyar bayan ya yi garkuwa da ita a watan Disamba, Daily Trust ta ruwaito.

A wata takardar da hadiminsa na fannin yada labarai, Sule Yau Sule ya fitar a shafin sa na Facebook, Shekarau ya jajanta wa iyayen yarinyar tare da shan alwashin sai ya bi mata khadin ta.

Sanata da ya yi gwamnan Kano har sau biyu, ya ce:

"Wannan kisan rashin imanin ba za mu bar shi ya tafi haka ba", inda ya sha alwashin bibiyar lamarin har sai ya ga karshen sa.

Shekarau ya yi fatan Allah ya bai wa iyayen Hanifa juriya da hakurin wannan rashin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel