Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai mummunan hari kan mutanen ƙauye, Sun bindige da dama

Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai mummunan hari kan mutanen ƙauye, Sun bindige da dama

  • Wasu yan ta'adda da ake zargin Fulani makiyaya ne sun halaka mutum biyu a wani sabon hari da suka kai ƙauyen jihar Ondo
  • Yan bindigan sun buɗe wa Manajan gidan man Fetur da yaronsa ɗaya wuta, kuma dukka mutum biyun sun mutu
  • Wani mazaunin ƙauyen da lamarin ya faru, ya bayyana cewa Manajan na gab da fita gidan man yayin da maharan suka iso

Ondo - Wasu yan ta'adda sun halaka aƙalla mutum biyu a wani mummunan hari da suka kai ƙauyen Okeluse dake ƙaramar hukumar Ose, jihar Ondo, ranar Lahadi da yamma.

Jaridar Punch ta rahoto cewa waɗan da suka mutu yayin harin sune, wani manajan gidan man Fetur da kuma m'aikacinsa.

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai mummunan hari kan mutanen ƙauye, Sun bindige da dama Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar wani shaidan gani da ido, maharan sun farmaki ƙauyen da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, kuma suka buɗe wa mutanen wuta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mayakan Boko Haram sun kara sace yan mata a sabon harin Chibok jihar Borno

Yadda lamarin ya faru

Wani mazaunin ƙauyen, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa, ya bayyana maharan da miyagun Fulani makiyaya masu kisa, waɗan da ake zargin suna aikata ta'addanci a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Cable ta rahoto mutumin Yace:

"Yan bindigan sun harbe wani mutum ɗaya daga cikin yaran dake siyar da mai a gidan mai, aka gaggauta kai shi Asibiti, amma ya mutu da safiyar Litinin."
"Manajan gidan man Fetur ɗin da suka bindige nan take ya mutu.Yana gab da fita daga gidan man tare da yaron nasa lokacin da maharan suka iso.

Shin yan sanda sun samu rahoton lamarin?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace zai fitar da cikakken bayani daga baya.

Wannan na zuwa ne makonni ƙalilan bayan wasu yan bindiga sun hallaka mutum biyar a ƙauyen Arimogija dake ƙaramar hukumar Ose, jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun bude wuta, sun yi awon gaba da Kwamishinan Jiha

A wani labarin na daban kuma Mutumin da ya kashe Hanifa yar shekara 5 a Kano, ya faɗi firar da suka yi ta karshe bayan ya shayar da ita guba ƙafin ta karisa mutuwa

Shugaban makaranta, Abdulmalik Tanko, wanda ya sace Hanifa kuma ya kashe ta, ya faɗi firar da suka yi kafin ta karisa mutuwa.

Malamin yace ya yi amfani da robar madara ta yara 'Bobo' wajen zuba wa Hanifa guba, kuma ya yaudareta ta sha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel