Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun je har gida, sun yi awon gaba da Kwamishinan Jiha

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun je har gida, sun yi awon gaba da Kwamishinan Jiha

  • Yan bindiga sun kutsa kai har cikin gidan kwamishina a jihar Bayelsa, sun yi awon gaba da shi zuwa cikin jeji
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki kauyen Otuokppoti da daddare, suka bude wuta domin tsorata mutane
  • Rundunar yan sandan jihar ta sanar da cewa tuni ta kaddamar da aikin ceto kwamishinan tare da kame maharan

Bayelsa - Miyagun yan bindiga sun sace kwamishinan cinikayya da kasuwanci na jihar Bayelsa, Mista Otokito Federal Oparmiola.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun yi awon gaba da Mista Otokito, a gidansa dake Otuokpoti, ƙaramar hukumar Ogbia, a daren ranar Alhamis.

Daily Trust ta rahoto cewa yan ta'addan sun farmaki garin ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Alhamis, bayan tsorata mutane, suka shiga gidan kwamishinan.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa mahaifiyar attajiri Dahiru Mangal, rasuwa

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun je har gida, sun yi awon gaba da Kwamishinan Jiha Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wata majiya daga hukumar yan sanda, ta bayyana cewa kwamishinan ya gane ɗaya daga cikin waɗan da suka sace shi, kuma ga dukkan alamu ɗan yankin su ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa aka sace kwamishinan?

Leadership ta ruwaito cewa, wasu mutanen na ganin sace kwamishinan ba zai rasa alaƙa da shirin da gwamnati take ta bankaɗo masu satar ɗanyen mai da kuma gudanar da haramtacciyar masana'antar tace mai.

A ɗaya bangaren kuma mutane na ganin cewa, sace babban mutumin, garkuwa ce ta neman kuɗin fansa da yan ta'adda suka maida sana'a a sassan Najeriya.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, yace maharan sun kutsa har cikin gidansa, suka tasa shi zuwa wani ɓoyayyen wuri da ba'a gano ba.

"Hukumar yan sanda ta kaddamar da aikin ceto kwamishinan, da kuma damƙe masu hannu a lamarin. Yanzun dai muna cigaba da bincike."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan harin rashin imani jihar Neja, sun halaka dandazon mutane

A wani labarin na daban kuma Sojojin Najeriya sun hallaka gawurtattun yan ta'adda da suke nema ruwa a jallo a jihar Filato.

Dakarun rundunar Sojin Operation Safe Haven sun samu nasarar ragargazan yan ta'adda uku da suke nema ruwa a jallo a jihar Filato.

Kakakin rundunar, Manjo Takwa, yace sojojin sun samu bayanan maɓoyar yan ta'addan, suka farmake su har suka bindige uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel