Da Dumi-Dumi: Boko Haram ta sake sace yan mata a sabon harin Chibok jihar Borno

Da Dumi-Dumi: Boko Haram ta sake sace yan mata a sabon harin Chibok jihar Borno

  • Mayakan kungiyar ta'addanci Boko Haram sun ƙara kai hari yankin ƙaramar hukumar Chibok dake jihar Borno
  • Wani mazaunin yankin da lamarin ya faru, ya bayyana cewa yan ta'addan sun yi awon gaba da yan mata da dama
  • Garin Chibok ya yi kaurin suna a duniya tun bayan sace ɗalibai mata sama da 200 a makarantar Sakandire da yan Boko Haram suka yi a shekarar 2014

Borno - Mayakan Boko Haram sun sake garkuwa da yan mata a sabon harin da suka kai wani yankin ƙaramar hukumar Chibok, dake jihar Borno.

Daily Trust ta rahoto cewa yan ta'adda sun farmaki garin ne ranar Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Mutane da dama sun tsere zuwa cikin jeji da kuma ƙauyukan da suka zagaye garin, yayin da yan ta'addan suka kai hari ƙauyen Femi, dake kusa da Chibok.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun bude wuta, sun yi awon gaba da Kwamishinan Jiha

Jihar Borno
Da Dumi-Dumi: Boko Haram ta sake sace yan mata a sabon harin Chibok jihar Borno Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mayakan kungiyar ta'addancin sun ƙone gidaje akalla 20 yayin harin, cikin su har da rashen cocin EYN.

Wani mazaunin ƙauyen da abun ya faru, Bitrus Yohanna, yace manufar yan ta'addan na kan shugaban yan bijilanti, saboda sun matsa wa Boko Haram a yankin.

Yohanna yace:

"Ranar Alhamis ta zama ta baƙin ciki a ƙauyen Pemi. Yan ta'addan sun zo da adadi mai yawa, suka fara ruwan alburusai, suka kama kwamandan yan Bijilanti, suka yanka shi ta maƙogwaro."
"Yan ta'addan sun kuma ƙone gidajen mutane da yawa, cikin su har da ginin cocin EYN."

Mutum nawa maharan suka sace?

Ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar Bijilanti, Ba'ana Musa, wanda yana ɗaya daga cikin waɗan da suka fafata da yan ta'addan, yace takwas daga cikin waɗan da suka sace sun kuɓuta

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan harin rashin imani jihar Neja, sun halaka dandazon mutane

Yace:

"Sun shigo da daddare, mafi yawan mutanen ƙauyen sun gudu zuwa cikin jeji. Mata takwas daga cikin waɗan da yan ta'addan suka sace sun kubuta, sun komo gida yau da misalin ƙarfe 11:00 na safe."
"Amma mun shiga matsanciyar damuwa kan batan yan matan. A yanzun da nake magana da ku, mafi ƙaranci sun sace yan mata 17."

Garin Chibok ya karaɗe duniya ne a shekarar 2014, lokacin da mayaƙan Boko Haram suka kai hari makarantar sakandiren mata dake garin, suka sace ɗalibai 276.

A wani labarin kuma Malamin da ya sace yarinya Hanifa Abubakar kuma ya kashe ta a Kano, ya faɗi firarsa da ita ta ƙarshe bayan ya shayar da ita guba

Shugaban makaranta, Abdulmalik Tanko, wanda ya sace Hanifa kuma ya kashe ta, ya faɗi firar da suka yi kafin ta karisa mutuwa.

Malamin yace ya yi amfani da robar madara ta yara 'Bobo' wajen zuba wa Hanifa guba, kuma ya yaudareta ta sha.

Kara karanta wannan

Dubun wasu gawurtattun yan leƙen asirin yan bindiga ya cika a Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel