Zamfara: Jama'a sun fada shagali da murna bayan sojoji sun ragargaza 'yan ta'adda a daji

Zamfara: Jama'a sun fada shagali da murna bayan sojoji sun ragargaza 'yan ta'adda a daji

  • Dakarun sojin Najeriya sun yi raga-raga da sansanin ‘yan bindiga da ke Gwashi, cikin karamar hukumar Bukkuyum da wasu bangarori na dajin Anka a jihar Zamfara
  • An samu bayanai akan yadda sojojin suka yi wa ‘yan bindigar suka taru a dajin Gando fata-fata tare da halaka su, sun kuma kwace shanaye da dama a hannun su
  • Mazauna kauyakun da ke kusa da inda sojojin suka yi ragargazar sun fito suna shagulgula akan nasarorin da sojin suka samu sakamakon karon battar su da ‘yan bindigan

Zamfara - Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar ragargazar ‘yan bindiga a sansanin su da ke Gwashi, karamar hukumar Bukkuyum da wasu bangarori na dajin Anka da ke jihar Zamfara inda suka amso shanaye da dama.

Gidan Talabijin din Channels ya tattaro bayanai a kan yadda ‘yan bindiga suka yi kawanya a dajin Gando inda sojin suka zagaye su suka halaka yawancin su.

Kara karanta wannan

Sabon harin ta'addanci: 'Yan bindiga sun afkawa sansanin sojoji a Katsina, sun yi barna

Zamfara: Jama'a sun fada shagali da murna bayan sojoji sun ragargaza 'yan ta'adda a daji
Zamfara: Jama'a sun fada shagali da murna bayan sojoji sun ragargaza 'yan ta'adda a daji. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mazauna kauyakun da ke kusa sun bayyana suna shagulgula a kan nasarar da sojojin suka yi yayin karon su da ‘yan bindigan.

‘Yan bindigan sun dade suna amsar haraji daga hannun mazauna karamar hukumar Bukkuyum tare da barazanar ganin bayan su matsawar ba su biya ba.

Har wasika ‘yan bindigan suka tura wa garuruwan Wawan Icce Salihu, Wawan Icce Ibrahim, Gangara, Gande, Tungar Gebe, Galle, Nan Narki, Ruwan Kura da ‘yar Galma da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.

A farkon watan Janairu, ‘yan bindigan su kai wa wasu kauyaku 4 farmaki a karamar hukumar Anka da Bukkuyum inda suka halaka fiye da mutane 50, Channelstv ta ruwaito.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alawadai a kan kisan a lokacin sannan ya lashi takobin ganin bayan ‘yan bindigan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da ke gudun ceto rai su na kai farmaki yankunan Zamfara, Dan majalisa

“Yan bindigan nan za su zama tarihi, ba za mu zauna ba har sai mun ga karshen ‘yan ta’addan da suka addabi mutanen gari, suna halaka wadanda basu ji ba basu gani ba,” a cewar Buhari a lokacin.
“Muna bukatar jama’an da harin ya shafa su kara hakuri yayin da muke mika ta’aziyyar mu ga ‘yan uwan wadanda lamarin ya shafa. Mun jajirce wurin ganin bayan duk wasu ‘yan ta’adda don kawo zaman lafiya a kasar nan.”

Nasara: Dakarun sojin Najeriya sun sheƙe ƴan ta'adda 49, 863 sun miƙa wuya, DHQ

A wani labari na daban, hedkwatar tsaron kasa ta ce ta halaka 'yan ta'addan 49 a karkashin ayyukan sojojin ta yayin da 'yan ta'addan 863 suka mika makaman su a makonni biyu da suka gabata.

Daraktan yada labarai, Bernard Onyeuko, ya sanar da hakan yayin bayar da bayani kan ayyukan sojojin a ranar Alhamis a Abuja, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara: Gwarazan sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutane

Onyeuko ya ce sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun halaka 'yan ta'adda 37, sun cafke 17 tare da samo miyagun makamai 117.

Asali: Legit.ng

Online view pixel