Zamu saka maka bisa abubuwan da ka yiwa jam'iyya, Tinubu ga dan takaran shugaban APC

Zamu saka maka bisa abubuwan da ka yiwa jam'iyya, Tinubu ga dan takaran shugaban APC

  • Sanata mai wakiltar Neja ta gabas ya samu goyon bayan babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu
  • Yayinda Tinubu ke neman kujeran shugaban kasa, Sanata Mohammed Sani ne neman kujeran shugaban jam'iyya
  • Tinubu ya kai masa ziyara inda yayi masa alkawarin biyansa bisa kokarin da ya yiwa jam'iyya a baya

Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress(APC) Asiwaju Bola Tinubu, da safiyar Asabar ya kai ziyara wajen daya daga cikin yan takaran kujeran shugabancin jam'iyyar.

Tinubu ya ziyarci Sanata Sani Musa, wanda shine shugaban kwamitin harkokin majalisar dattawa a gidansa dake unguwar Maitama Abuja, TheNation ta ruwaito.

Ya yi bayanin irin gudunmuwar da Sanatan ya baiwa jam'iyyar APC kuma ya yi alkawarin zasu saka masa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Tinubu na ci gaba da zawarci, ya ziyarci babban jigo na APC

A cewar Tinubu:

"Sadaukarwan da Sanata Mohammed Sani Musa ya yiwa jam'iyyar All Progressives Congress(APC) a 2014/2015 ba zai tafi a banza ba, shugabannin APC na sane da hakan. Zamu saka masa."

Zamu saka maka bisa abubuwan da ka yiwa jam'iyya, Tinubu ga dan takaran shugaban APC
Zamu saka maka bisa abubuwan da ka yiwa jam'iyya, Tinubu ga dan takaran shugaban APC
Asali: Facebook

Ni ba kujeran Shugaban kasa nike nema ba, kujeran Shugaban APC nike so: Ali Modu Sherrif

Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sherrif, a ranar Juma'a ya bayyana cewa ko kadan bai da niyyar neman kujerar shugaban kasa, kujeran Shugaban jam'iyya yake nema.

Ali Sherrif na cikin jerin masu neman kujerar shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a taron gangamin da za'a yi ranar 26 ga Febrairu, 2022.

A hirar da yayi da manema labarai a birnin tarayya Abuja, yace ba tsoron neman kujerar shugaban kasar yake ba amma dai ba ita yake so ba, rahoton TheNation.

Kara karanta wannan

Ba zan taba komawa jam'iyyarku ba, Obasanjo ya bayyanawa jiga-jigan PDP

Jam'iyyar APC ta fitar da jadawalin abubuwan da za su faru nan da gangaminta na kasa

Jam’iyyar APC ta ce za ta fara siyar da fom ga masu neman tsayawa takarar mukamanta na kasa gabanin babban taron kasa daga ranar 14 ga watan Fabrairu.

John Akpanudoedehe, sakataren jam’iyyar APC na kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel