Ni ba kujeran Shugaban kasa nike nema ba, kujeran Shugaban APC nike so: Ali Modu Sherrif

Ni ba kujeran Shugaban kasa nike nema ba, kujeran Shugaban APC nike so: Ali Modu Sherrif

  • Tsohon shugaban jam'iyyar PDP yana neman takaran kujeran shugabancin jam'iyyar APC
  • Ali Modu Sherrif ya bayyana cewa babu wanda ya kaishi cancantan kujeran shugaban APC cikin yan takara
  • Ya yi watsi da maganganun masu cewa kujeran Shugaban kasa yake nema

Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sherrif, a ranar Juma'a ya bayyana cewa ko kadan bai da niyyar neman kujerar shugaban kasa, kujeran Shugaban jam'iyya yake nema.

Ali Sherrif na cikin jerin masu neman kujerar shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a taron gangamin da za'a yi ranar 26 ga Febrairu, 2022.

Ali Modi Sherrif
Ni ba kujeran Shugaban kasa nike nema ba, kujeran Shugaban APC nike so: Ali Modi Sherrif Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

A hirar da yayi da manema labarai a birnin tarayya Abuja, yace ba tsoron neman kujerar shugaban kasar yake ba amma dai ba ita yake so ba, rahoton TheNation.

Kara karanta wannan

2023: Daga ƙarshe, Yahaya Bello ya sanar cewa ya shiga jerin masu son gadon kujerar Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Ina son bayyanawa, ba na neman kujeran shugaban kasa. Shugabancin uwar jam'iyya nake nema saboda in taya jam'iyyar samun nasara."
"Ina son jagorantar yakin neman zabe kamar yadda muka yi a 2014 don tabbatar da cewa babanmu kuma shugabanmu ya mika mulki ga dan APC."
"Idan ina son zama shugaban kasa, bana tsoron kowa amma ban son shugaban kasa, shugaban jam'iyya nike so."

Jam'iyyar APC ta fitar da jadawalin abubuwan da za su faru nan da gangaminta na kasa

Jam’iyyar APC ta ce za ta fara siyar da fom ga masu neman tsayawa takarar mukamanta na kasa gabanin babban taron kasa daga ranar 14 ga watan Fabrairu.

John Akpanudoedehe, sakataren jam’iyyar APC na kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

Orji Kalu: Duk inyamurin da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 bai san me yake ba

A cewarsa:

"CECPC na jam'iyyar APC a taronta na yau da kullum karo na 19 a ranar Laraba 19 ga Janairu, 2022 a sakateriyar jam'iyyar ta kasa ta yi nazari tare da zartar da jadawalin ayyuka na Fabrairu 26 na taron gangamin jam'iyyar APC."

Asali: Legit.ng

Online view pixel