Sojoji sun kashe hatsabiban masu garkuwa da mutane a Plateau, sun ƙwato makamai

Sojoji sun kashe hatsabiban masu garkuwa da mutane a Plateau, sun ƙwato makamai

  • Rundunar Operation Safe Heaven (OPSH) yayin kokarin ta na samar da zaman lafiya a Jihar Plateau wasu yankunan jihar Kaduna da Bauchi ta halaka masu garkuwa da mutane 3 a Filato
  • Kakakin rundunar OPSH, Manjo Ishaku Takwa a wata takarda da ya saki jiya ya bayyana yadda suka samu nasarar halaka shu’uman wadanda ake zargin sun tsero daga gidan yari a ranar 28 ga watan Nuwamban 2021
  • An gano cewa masu garkuwa da mutanen ne suka addabi garin da satar jama’a, hakan yasa rundunar OPSH ta yi musu kwanton bauna, bayan tirke su ta yi gaggawar halaka su tare da kwace makamai da dama

Plateau - Rundunar OPSH yayin kokarin ganin ta samar da zaman lafiya a jihar, wasu yankunan Jihar Kaduna da Jihar Bauchi ta samu nasarar halaka wasu masu garkuwa da mutane 3 a Jihar Plateau inda ta kwace makamai a hannun su, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojojin Najeriya sun hallaka gawurtattun yan ta'adda da suke nema ruwa a jallo

Sojoji sun kashe hatsabiban masu garkuwa da mutane a Plateau, sun ƙwato makamai
Sojoji sun ragargaji masu garkuwa da mutane a Plateau, sun kwato makamai. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Kakakin rundunar OPSH, Manjo Ishaku Takwa a wata takarda da ya saki jiya ya ce jami’an rundunar sun samu nasarar ragargazar wadanda ake zargin suna cikin ‘yan gidan yarin da suka tsero a ranar 28 ga watan Nuwamban 2021.

Har miyagun makamai aka kwace a hannun su

Kamar yadda The Guardian ta ruwaito takardar ta zo:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Rundunar Operation Safe Heaven (OPSH) bayan samun bayanan sirri ta yi nasarar ragargazar wasu masu garkuwa da mutane a Plateau. Suna cikin wadanda OPSH ta ke nemo ido rufe saboda zarginsu da zama wadanda su ke shirya garkuwa da mutane a Plateau.
“Rundunar ta dade tana bincike da nazari akan yankin Gyero, inda ake zargin masu garkuwa da mutane suna harkokin su. Bayan masu garkuwa da mutanen sun lura da sojojin, sun yi gaggawar bude musu wuta. Cikin kwarewa rundunar ta mayar musu da wutar.

Kara karanta wannan

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

“Cikin makaman da aka kwace a hannun su akwai AK-47, magazin na AK-47 guda biyu da sauran miyagun makamai. Sannan an samu nasarar amsar Keke Napep daya, waya kirar Itel daya, waya kirar Tecno daya, kaifafan wukake biyu da hulunan sojoji.”

Kwamandan rundunar ya yaba wa sojojin akan jajircewar su

Takardar ta kara da bayyana yadda kwamandan rundunar OPSH, Manjo Janar Ibrahim Ali ya yaba da ayyukan rundunar inda yace hakan zai razanar da masu garkuwa da mutane da sauran miyagun mutane da ke cikin Jihar.

Janar Ali ya bukaci mazauna Jihar da su kasance masu ba jami’an tsaro hadin kai kuma su yi gaggawar kai wa ‘yan sanda rahoto da zarar sun kula da wani abin zargi kusa da su.

Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla fararen hula uku ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai hari a kauye da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno da yammacin ranar Jumma'a.

Kara karanta wannan

An kuma: An sake yin garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato

Kungiyar yan ta'addan sun afka kauyen Kautikari da ke kusa da gari Chibok misalin karfe 4 na yamma, suna harbe-harbe ba kakkautawa kuma suka kona gidaje da dama a cewar majiyoyi na tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyar, maharan sun iso ne a cikin motocci guda biyar dauke da bindiga mai harbo jiragen yaki kuma suka shigo cikin sauki ba tare da an nemi taka musu birki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164