Nasrun Minallah: Sojoji sun bindige gawurtattun yan bindiga da suke nema a Filato

Nasrun Minallah: Sojoji sun bindige gawurtattun yan bindiga da suke nema a Filato

  • Dakarun rundunar Sojin Operation Safe Haven sun samu nasarar ragargazan yan ta'adda uku da suke nema ruwa a jallo a jihar Filato
  • Kakakin rundunar, Manjo Takwa, yace sojojin sun samu bayanan maɓoyar yan ta'addan, suka farmake su har suka bindige uku
  • Kwamandan Operation Safe Haven, ya yaba wa sojojin tare da gargaɗin duk wani ɗan ta'adda ya bar cikin jihar Filato

Plateau - Dakarun Operation Safe Haven sun hallaka wasu masu garkuwa uku da suka jima suna addabar mutane da ayyukan ta'addanci a jihar Filato.

Jaridar Punch tace sojojin sun bindige yan ta'addan ne a yankin Gyero, dake ƙaramar hukumar Jos ta Kudu, tare da kwato makamai da suka haɗa da bindigun AK-47 da alburusai.

Sojan Najeriya
Nasrun Minallah: Sojoji sun bindige gawurtattun yan bindiga da suke nema a Filato Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar Operation Safe Haven, Ishaku Takwa, shi ne ya tabbatar da aika mutanen lahira a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Nasara: Dakarun sojin Najeriya sun sheƙe ƴan ta'adda 49, 863 sun miƙa wuya, DHQ

Leadership ta rahoto kakakin rundunar yace:

"Bayan samun wasu sahihan bayanai, dakarun sojin Operation Safe Haven, sun lalata tare da kashe gawutattun tawagar yan bindiga a Filato."
"Yan ta'addan sun jima a cikin jerin waɗan da rundunar take nema ruwa a jallo, kuma an yi imanin su ke jagorantar hare-haren kwanan nan a faɗin jihar."
"Yan ta'addan waɗan da suka kware a garkuwa da mutane sun gamu a ajalin su ne yayin da sojoji suka bibiye su a Gyero, wurin da suke shirya ayyukan ta'addancin su."

Yadda aka kashe yan ta'addan

Kakakim sojojin ya ƙara da cewa lokacin da yan ta'addan suka ga zuwa dakarun sojin, sai suka buɗe musu wuta, amma sojin suka maida martani kuma suka ci ƙarfin su.

"Sojojin sun maida martani inda aka yi musayar wuta amma suka ci ƙarfin su, suka hallaka shahararrun yan ta'adda uku."

Kara karanta wannan

Kebbi: Rayuka 15 ne suka salwanta a farmakin ƴan ta'adda, Jami'ai

"Daga cikin makaman da sojojin suka kwato sun haɗa da, bindigar AK-47, carbin alburisai, Keke Napep da sauran su."

Kwamandan Operation Safe Haven, Manjo Janar Ibrahim Ali, ya gargaɗi duk wani ɗan garkuwa ya fice daga jihar Filato ko kuma ya haɗu da ajalinsa.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai mummunan harin rashin imani jihar Neja, sun halaka dandazon mutane

Yan bindigan sun kai mummunan hari ƙauyen Bobi dake jihar Neja, inda suka kashe dandanzon mutanen da ba'a gano adadin su ba zuwa yanzu.

Da farko maharan sun shiga kasuwar Nkuru, yayin da mutane yan kasuwa da masu siya ke gudanar da harkokinsu, amma ƙarar harbin bindiga ta sanya kowa ya watse daga kasuwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel