Tsadar rayuwa a 2021: Yadda hauhawar farashin kayayyaki ya kasance a kowane wata

Tsadar rayuwa a 2021: Yadda hauhawar farashin kayayyaki ya kasance a kowane wata

  • Shekarar 2021 ta kare, masana na ta hasashen abubuwan da ka iya faruwa na sauyi a shekarar 2022 da muka shiga
  • Tsadar kayayyaki na daga cikin abubuwan da 'yan Najeriya suka yi fama dashi a 2021, yanzu ana cikin 2022 ko ya za ta kasance?
  • Idan muka waiwaya baya, rahoto ya bayyana yadda kowace a 2021 ta zo da nata kason hauhawar farashin kayayyaki

A shekarar da ta gabata, 'yan Najeriya sun sha kokawa kan yadda tsadar rayuwa ta dabaibaye kasuwanni, lamarin da ya kai ga gwamnati ta tsoma baki kan ba 'yan kasa hakuri.

'Yan Najeriya na fatan ganin sauki a ko da yaushe, sai dai, masana sun yi tsokaci cewa, za a ci gaba da fuskantar tsadar abinci.

Kara karanta wannan

Mai shari'a ta caccaki DSS, ta ce ka da su kara kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya daya

A wani bangare guda, babban bankin Najeriya ya yi hasashen samun saukin wajen farashin kayayyaki a kasar, kamar yadda BBC ta tattaro.

Hauhawar farashi a 2021
Tsadar rayuwa a 2021: Yadda hauhawar farashi ya kasance kowace a 2021 | Hoto: TheCable
Asali: UGC

Sai dai, masana tattalin arziki a kasar nan na gargadin cewa zai yi matukar wuya a iya cimma hasashen da babban bankin kasar CBN ya yi na sa ran saukar farashin kayayyaki.

Babban bankin ya yi hasashen cewa a 2022, farashin kayan abinci zai sauka da 10% cikin 100%, saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da kuma rashin bin matakan da suka kamata.

Kasimu Garba Kurfi, wani masanin tattalin arziki da ke birnin Legas, yana cikin masu irin wannan ra'ayi na cewa hasashen CBN ba zai tabbata ba.

Lura da haka, wannan rahoton ya tattaro daga majiya yadda farashin kayayyaki ya kasance a 2021, kamar yadda TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Jerin yadda hauhawar farashin kaya a cikin 2021 ya kaya

  1. Janairu: 16.47%
  2. Fabrairu: 17.33%
  3. Maris: 18.17%
  4. Afrilu: 18.12%
  5. Mayu: 17.93%
  6. Yuni: 17.75%
  7. Yuli: 17.38%
  8. Agusta: 17.01%
  9. Satumba: 16.63%
  10. Oktoba: 15.99%
  11. Nuwamba: 15.40%
  12. Disamba: 15.63%

Matsakaici farashi a watanni 12: 16.95%

A wani kabarin, jam’iyyar PDP ta mayar da martani kan kaddamar da dalar shinkafa a Abuja da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, inda tace ba komai ba ne face karya, Channels Tv ta rahoto.

Jam’iyyar ta adawa a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, ta ce jam’iyyar APC ta tara kafafen yada labarai ne don yaudarar ‘yan Najeriya gabanin zaben 2023.

Hakazalika, sanarwar ta kuma bayyana yadda jam'iyyar APC ke sanya duniya na yiwa shugaba Buhari dariya bayan matsin da 'yan kasa ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel