Magidanci ya gwangwaje mijin tsohuwar matarsa da kyauta, bidiyon su ya taba zukata

Magidanci ya gwangwaje mijin tsohuwar matarsa da kyauta, bidiyon su ya taba zukata

  • Wani mutum ya birge mutane da dama a kafafen sada zumunta akan yadda ya kyautata wa mijin tsohuwar matarsa
  • Mutumin ya siya wa mijin tsohuwar matarsa wasu takalma masu ban sha’awa a matsayin kyautatawa saboda kula masa da yaransa da ya yi
  • Ya kuma nuna jin dadinsa akan irin kyakkyawar alakar da mutumin ya gina tsakaninsa da yaransa duk da ba shi bane mahaifinsu

Wasu maza biyu sun zama ababen kwatance bayan irin yadda su ka nuna kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu wacce ba a samu a wurin maza sai dai dai.

Daya yana auren wata mata ne wacce tsohuwar matar dayan ce, amma kyakkyawar alakar ta su sai da ta ba mutane da dama mamaki.

Magidanci ya gwangwaje mijin tsohuwar matarsa da kyauta, bidiyon su ya taba zukata
Magidanci ya gwangwaje mijin tsohuwar matarsa da kyauta, bidiyon su ya taba zukata. Hoto daga @kla365
Asali: Instagram

Cikin jin dadi ya siya wa mijin tsohuwar matarsa wani takalmi mai kyau da kuma kayatarwa.

Kara karanta wannan

Bidiyon dan achaba dauke da fasinjoji 7 reras ya janyo cece-kuce

Har zubar da hawaye mutumin ya yi a wani bidiyo wanda tsohuwar matarsa ta wallafa a Instagram, inda aka ga yadda mutumin ya ke godiya ga mijin tsohuwar matarsa tare da wasu yara da ake zargin yaransa ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ga mutumin ya na wakar yabo ga mijin tsohuwar matarsa wacce ta sa mutumin ya zauna yana mamaki.

Ya yaba da yanayin fahimtar mijin da kuma gina alaka mai kyau tsakaninsu tare da ba shi damar zama da yaransa ba tare da wata takura ba.

Daga bisani ya mika wa mijin tsohuwar matar tasa wata kyauta wacce cikinta akwai wani takalmi wanda hakan ya sa mijin matar ya yi saurin mikewa ya amsa tare da rungume sa.

Jama'a sun yi martani

Nan da nan jama'a suka yi ca inda wasu suka dinga yaba irin kyakyawar alakar da ke tsakanin mazan biyu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Sarkin Bauchi yana rera wakar yabo yayin da ya karbi bakuncin Kiristoci a fadarsa

@schoolboy_yu yace:

"A gaskiya hankalin naku ya kai duk inda ya ke. Dukkan maza a kowanne shekaru suke kuwa a rayuwa za su iya koyon darasi daga wannan bidiyon."

@robertbobbyfai yace:

"Hakkun! Wannan tunatarwa ce ga bakaken maza, iyaye maza bakar fata ya dace su yi murna tare da godewa junansu ba tare da duban wasu abubuwa na iyalai ba."

Bidiyon dan achaba dauke da fasinjoji 7 reras ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, wani dalili na iya janyo wa mutum ya kirkiro abinda ba a taba gani ba, amma wannan kirkirar babur din na musamman ya shayar da mutane da dama tsananin mamaki.

A wani bidiyo wanda ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani, an ga yadda wani mutum ya ke tuka wani babur mai doguwar kujera.

Shafin goldmynetv ya wallafa bidiyon a Instagram, kum an ga wani babur da zai iya daukar mutane 8 inda daya zai kasance mai tuki yayin da sauran wurin zai isa fasinjoji 7 duk a lokacin guda.

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

Asali: Legit.ng

Online view pixel