Yadda Gwamnatin Buhari ta taimakawa mutane sama da 500, 000 inji Dr. Isa Pantami

Yadda Gwamnatin Buhari ta taimakawa mutane sama da 500, 000 inji Dr. Isa Pantami

  • Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce gwamnati ta taimakawa dubban mutane da hanyar neman na-kansu
  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na kasa ya fi bada karfi wajen samun kwarewar aiki
  • Gwamnatin Buhari ta na hada-kai da kamfanonin Duniya domin a koyawa ‘yan Najeriya sana’a

Abuja - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce gwamnatin tarayya ta taimakawa mutane da hanyoyin neman na-kai.

A ranar Alhamis, 20 ga watan Junairu 2022, Punch ta rahoto Isa Ali Ibrahim Pantami ya na cewa mutum sama da 500, 000 suka amfana da tsare-tsarensu.

Ministan ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya fitar ta bakin hadimarsa, Uwa Suleiman a wajen wani taron koyon sana’a da bankin Duniya ya shirya.

Kara karanta wannan

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

Mai girma Ministan ya nemi hadin-kai da taimakon bankin Duniya da sauran kungiyoyi, ya kuma fadi kokarin da ma’aikatarsa tayi wajen bunkasa tattali.

Ba ta satifiket ake yi ba - FG

“Mu na kokarin maida hankali a kan sanin makaman aiki, musamman na yanar gizo a kan tara takardun shaidar karatu ba tare da iya aikin hannu ba.”
Dr. Isa Pantami
Isa Ali Ibrahim Pantami Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Ba za a iya samun tattalin arziki na zamani a cikin rumbuna ba, shiyasa gwamnatin tarayya ta ke hada-kai da manyan kamfanonin zamani na Duniya.”

Ministan yake cewa ana yin hakan ne domin a karfafa al’umma, a koya masu aiki ta yadda za su rika daukar ma’aika a karon kansu, basu zauna jiran aiki ba.

Jaridar ta ce bankin Duniya ya shiga yarjejeniya da gwamnatin tarayya ta karkashin ma’aikatan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed

Ana ganin amfanin shirin NDEPS

Hadin kan da ake samu tsakanin kamfanonin zai taimakawa Najeriya da koyon aiki a kokarinta na samun masu aikin hannu kamar yadda yake a tsarin NDEPS.

A watan Nuwamban 2019 ne Mai girma shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da tsarin na National Digital Economy Policy & Strategy a Najeriya.

An kara kudin fetur?

A jiya ne aka ji ashe jita-jitar cewa majalisar tattalin arziki ta kasa watau NEC ta amince a kara farashin man fetur zuwa sama da N300 sam ba gaskiya ba ne.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya karyata wadannan rahotanni. ya ce kawo yanzu NEC ba ta dauki matsaya ba tukun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel