A yanzu haka: Mayakan Boko Haram sun shiga Chibok, su na luguden wuta

A yanzu haka: Mayakan Boko Haram sun shiga Chibok, su na luguden wuta

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun kutsa wani kauyen karamar hukumar Chibok mai suna Pemi inda suke ta luguden wuta
  • Wani mai gadi ya tabbatar da hakan inda ya ce farar hula su na ta gudun ceton rai sakamakon harbin da 'yan ta'addan ke yi
  • A cewar mai bayar da labarin, 'yan ta'addan sun shiga kauyen ta wani daji makusanci, hakan yasa jama'a ke ta gudun ceton rai

Borno - Mayakan ta'addancin Boko Haram a halin yanzu suna cikin wani kauye a karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.

Wani mai gadi a yankin ya tabbatar wa da Daily Trust inda ya ce farar hula suna ta barin gidajen su.

A yanzu haka: Mayakan Boko Haram sun shiga Chibok, su na luguden wuta
A yanzu haka: Mayakan Boko Haram sun shiga Chibok, su na luguden wuta
Asali: Original
"Sun zo wurin karfe 7 na yamma kuma sun shiga kauyen Pemi, wanda ke da nisan kilomita 15 daga asalin garin Chibok.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta titsiye Supo Shasore, tsohon kwamishinan Legas kan damfarar P&ID

“Sun bayyana ne ta wani daji na kusa kuma sun fara harbi babu kakkautawa ta kowanne sashi bayan isowar su.
"Mutane da yawa sun shiga daji; wasu a halin yanzu suna cikin garin Chibok," majiyar ta ce.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel