A kara farashin litan mai zuwa N302 nan da Febrairu, kwamitin El-Rufa'i ta bada shawara

A kara farashin litan mai zuwa N302 nan da Febrairu, kwamitin El-Rufa'i ta bada shawara

  • Kwamitin da majalisar tattalin arzikin tarayya ta nada ta bada jerin shawarin yadda za'a samu kudin shiga
  • Daga cikin shawarin shine gwamnatin tarayya tayi gaggawar cire tallafin mai kuma farashin litan mai ya koma N302
  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke jagorancin majalisar tattalin arzikin tarayya NEC kuma gwamnoni ne mambobi

Abuja - Majalisar tattalin arzikin Najeriya NEC ta baiwa gwamnatin tarayya shawarar a kara farashin litan man fetur zuwa N302 nan da watan Febrairu 2022.

Wannan shawara na cikin jeringiyar shawarin da kwamitin NEC mai tattaunawa da kamfanin mai NNPC kan farashin man da ya kamata a sanya a Najeriya ta bada, rahoton TheCable.

Wannan kwamiti dake karkashin jagorancin gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ta gabatar da shawarin.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Buhari yace min bai sa kowa kara farashin man fetur ba: Shugaban majalisa

A 2021, NEC karkashin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ta nada kwamitin sakamakon rashin kudi.

A kara farashin litan mai zuwa N320 nan da Febrairu
A kara farashin litan mai zuwa N320 nan da Febrairu, kwamitin El-Rufa'i ta bada shawara Hoto: NEC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Gwamnan Godwin Obaseki an Edo, David Umahi na Ebonyi, da Kayode Fayemi na Ekiti.

Sauran sune Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, Shugaban NNPC, Mele Kyari da Ministan kudi, Zainab Ahmed Shamsuna.

Zaku tuna cewa a watan Oktoba, Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed ta sanar da cewa gwamnatin tarayya zata cire tallafin mai bayan rabin shekarar 2022.

A cewarta, za'a baiwa talakawan Najeriya milyan arba'in kudi dubu biyar-biyar matsayin kudin mota don rage radadin karin da farashin man zai yi.

Buhari yace min bai sa kowa kara farashin man fetur ba: Shugaban majalisa

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai ba kowa umurnin kara farashin man fetur ta hanyar cire tallafin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Kotun afil ta zabi ranar zama kan shari'ar dake tsakanin tsagin APC na Shekarau da Ganduje

Ahmad Lawan ya bayyana hakan ne yayin hirarsa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ranar Talata, 18 ga Junairu, 2022, rahoton DailyTrust.

Yace yana farin cikin fadawa yan Najeriya cewa Buhari bai sa kowa cire tallafin mai ba.

Yace:

"Ina farin cikin sanarwa yan Najeriya cewa shugaban kasa bai fadawa kowa a cire tallafin man fetur ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel