Ba a taba ba: Atiku ya shiga damuwa, ya ce bai taba ganin irin matsalar da Najeriya ke ciki ba

Ba a taba ba: Atiku ya shiga damuwa, ya ce bai taba ganin irin matsalar da Najeriya ke ciki ba

  • Kalubalen da Najeriya ke fuskanta dai na damun tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar
  • A cewar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kasar ba ta taba shiga mummunar matsala kamar haka ba
  • Atiku ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron tattaunawa na Daily Trust karo na 19 da ke gudana

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya koka da kalubalen da Najeriya ke fuskanta a yanzu.

A cewar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kasar nan ba ta taba samun kanta a irin wannan matsala mara kan gado ba.

Atiku ya shiga damuwa kan matsalolin Najeriya
Ban taba ganin irin halin nan ba: Atiku ya tausayawa 'yan Najeriya ganin halin da ake ciki | Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Abubakar ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa na Daily Trust karo na 19 da ke gudana a dakin taro na NAF Conference Centre and Suites, dake kan titin Gwarinpa, kusa da NEXT Shopping Mall, Kado da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Hotunan makusancin ɗan ta'adda Turji, tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura

Taken tattaunawar da ke gudana dai shi ne ‘2023: Siyasa, Tattalin Arziki da Rashin Tsaro’.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Ban taba ganin kasar nan tana fuskantar manyan kalubale ba tun kafuwarta kamar yadda nake gani a wannan lokaci."

Sarkin Musulmi: Rashin tsaro shine matsalar kasar nan, shi yasa muka gagara ci gaba

Sarkin musulmi na Sokoto, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya bayyana yadda matsalolin tsaro suka zama babbar matsala ga Najeriya.

Ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust ta safiyar yau Alhamis.

Legit.ng ta sanya ido kan tattaunawar, inda sarkin musulmin ke tsokaci kan yadda tsaro ke da muhimmaci ga ci gaban al'umma.

A wani labarin daban, gwamnoni 36 na tarayyar Najeriya sun amince su tattauna da shugabannin kungiyoyin NLC na ‘yan kwadago da na ‘yan kasuwa watau TUC.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mutane sun shiga daji sun kwato Sarkin su da yan bindiga suka sace a Filato

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnonin jihohin za su yi wannan zama ne a dalilin shawarar da suka ba gwamnatin tarayya na cewa a kara farashin litar fetur.

Shugaban kungiyar gwamnoni na kasa, Dr. Kayode Fayemi ya zanta da manema labarai bayan wani zama da gwamnonin suka yi a birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel