Man fetur: Gwamnoni za su yi zama da ‘yan kwadago a kan batun kai farashi N302

Man fetur: Gwamnoni za su yi zama da ‘yan kwadago a kan batun kai farashi N302

  • Shugaban kungiyar gwamnoni, Kayode Fayemi ya ce za su zauna da ‘yan kwadago da ‘yan kasuwa
  • Gwamnan jihar Ekiti ya shaidawa manema labarai cewa NGF za ta tattauna da wakilan NLC da TUC
  • Dr. Kayode Fayemi ya bayyana cewa za ayi taron ne da nufin warware batun karin kudin man fetur

Abuja - Gwamnoni 36 na tarayyar Najeriya sun amince su tattauna da shugabannin kungiyoyin NLC na ‘yan kwadago da na ‘yan kasuwa watau TUC.

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnonin jihohin za su yi wannan zama ne a dalilin shawarar da suka ba gwamnatin tarayya na cewa a kara farashin litar fetur.

Shugaban kungiyar gwamnoni na kasa, Dr. Kayode Fayemi ya zanta da manema labarai bayan wani zama da gwamnonin suka yi a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun zugo ‘Yan Majalisa su bankara Buhari a kan gyara dokar zabe

Da yake bayani a ranar Laraba, Mai girma gwamnan Ekiti, Fayemi ya ce zamansu da NLC da TUC zai sa a magance matsalar ba tare da jama’a sun ji haushi ba.

“Gwamnoni sun tattauna a kan batun cire tallafin fetur, kuma sun gama magana cewa za a zauna da shugabannin kungiyoyin NLC da TUC.”
“Za a zauna da nufin shawo kan lamarin ba tare da an samu rashin jin dadi ba, sai don nufin ceto tattalin arziki da mutanen Najeriya a karshe.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnoni
Gwamnoni a taron NGF Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

“Saboda haka za mu zauna da shugabannin NLC domin tabbatar da cewa a karshe an yi adalci wajen tattaunawar da mu, an kuma yi wa kowa gaskiya.”

Har ila yau, an ji cewa gwamnoni sun yabawa majalisar dattawa da ta gyara kudirn zabe, ta yi kwaskwarima a kan wuraren da ake ganin za su jawo cikas.

Kara karanta wannan

Zamfara: Matawalle ya ce suna shirin tona asirin masu aiki tare da ƴan ta'adda

Fayemi ya yi kira a madadin sauran gwamnonin jihohi, yana mai fatan majalisar wakilan tarayya za ta yi irin abin da Sanatocin suka yi ga kudirin gyaran zaben.

Rahoton ya bayyana cewa shugabannin TUC za su yi zama yau Alhamis domin su cin ma matsaya a kan wannan magana da gwamnonin suka bijiro da shi.

Farashin fetur zai tashi?

Gwamnoni su na so gwamnatin Muhammadu Buhari ta cire tallafin man fetur domin kudin da ake rabawa tarayya da kuma jihohi daga asusun FAAC ya karu.

Hakan zai jawo litar man fetur ya tashi daga tsakanin N162 da N165 zuwa sama da Naira 300.

Asali: Legit.ng

Online view pixel