Almundahanar N29bn: Kotu ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan Adamawa da dansa kan dakatar da kara

Almundahanar N29bn: Kotu ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan Adamawa da dansa kan dakatar da kara

  • Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da Vice Admiral Muritala Nyako da dansa, Abdulaziz Nyako suka daukaka a gabanta kan zargin naira biliyan 29 da ake tuhumarsu a kai
  • Sun nemi kotu ta kori shari'ar da EFCC ke yi da su kan almundahana cewa shaidar da hukumar ta gabatar bai alakanta su da aikata laifukan da ake zarginsu ba
  • Sai dai kotu ta yin watsi da hakan inda ta ce lallai su je su kare kansu a gaban kotu

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Vice Admiral Muritala Nyako da dansa, Abdulaziz Nyako sun sha kaye a kokarinsu na hana ci gaba da shari'ar almundahanar naira biliyan 29 da gwamnatin tarayya ke yi da su.

Kotun daukaka kara a Abuja ta yi watsi da karar da suka daukaka na neman a soke shari'ar da ake yi da su na zamba kan hujjar cewa shaidar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gabatar bai alakanta su da aikata laifukan da ake zarginsu da aikatawa ba.

Almundahanar N29bn: Kotu ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan Adamawa da dansa kan dakatar da kara
Almundahanar N29bn: Kotu ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan Adamawa da dansa kan dakatar da kara Hoto: Thisday
Asali: UGC

A hukuncinsa, kwamitin mutum uku na alkalan kotun daukaka kara, ya umurci tsohon gwamnan na Adamawa da dansa su je su kare kansu a shari'ar da ake yi da su, rahoton Channels TV.

Justis Olabisi Ige wanda ya karanto a madadin kwamitin ya riki cewa daga shaidar baka har na takardu da EFCC ta gabatar a kan su suna da inganci kuma sun alakanta su da zargin zamba.

Kotun daukaka karar ta ce karar da tsohon gwamnan da dansa suka shigar ba ta da wani tasiri, wanda ya cancanci kora kuma aka yi watsi da shi, Premium Times ta kuma rahoto.

Kotun ta umarce su da su koma babban kotun tarayya da ke Abuja sannan su tabbatar da cewa ba su da hannu a laifuffuka 37 da ake tuhumarsu da aikatawa.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Nyako da dansa a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja kan tuhume-tuhume 37 da suka shafi zamba da suka kai N29bn.

Bayan shekaru 14, an cigaba da shari'ar wawurar kudaden da tsohon gwamnan arewa ya yi

A wani labarin kuma, mun ji cewa an cigaba da shari'ar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Saminu Turaki a babbar kotun tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, bayan shekaru goma sha hudu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Turaki ya bayyana a gaban kotun a ranar 7 ga watan Disamba inda ya ke fuskantar zargi 32 kan wawurar wasu kudi da suka kai N36 biliyan.

A shekarar 2007, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta damke tshon gwamnan kuma ta gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Mai shari'a Binta Murtala Nyako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel