Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro yayin da kotu za ta yanke hukunci tsakanin Kanu da gwamnati

Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro yayin da kotu za ta yanke hukunci tsakanin Kanu da gwamnati

  • A yau ne ake zaman shari'a tsakanin Nnamdi Kanu da gwamnatin Buhari bisa wasu batutuwan da Kanu ya shigar kotu
  • Idan baku manta ba, an kamo Kanu daga wata kasar waje, an kawo shi Najeriya domin fuskantar shari'a kan cin amanar kasa
  • Ya zuwa yanzu, an daga karar sau da dama, inda a bangaren da gwamnati ke kara ta kara yawan tuhume-tuhume kan Kanu

Abia - Jami’an tsaro dauke da muggan makamai sun tare hanyoyin da ke kaiwa harabar babbar kotun jihar Abia da ke kan titin Ikot Ekpene a Umuahia yayin da kotu za ta yanke hukunci a yau kan karar da shugaban IPOB, Mazi Nnamdi ya shigar kan gwamnatin tarayya.

Tun da karfe 7:00 na safe, an baza jami'an tsaro a kusa da harabar kotun, Vanguard ta rahoto.

Nnamdi Kanu da gwamnatin Buhari
Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro yayin da kotu za ta yankewa Nnamdi Kanu hukunci | Hot GettyImages
Asali: UGC

Haka kuma an killace dukkan hanyoyin da ke kai wa ga kotun, wanda hakan ya tilastawa masu ababen hawa da masu tafiya a kafa bin wasu hanyoyin daban-daban.

An bukaci ‘yan jarida da ma’aikatan kotun da kuma mutanen da ke shiga harabar da su fito da katin shaida kafin a basu damar shiga harabar.

Alkalin kotun, Mai shari’a Benson Anya ya ce a zaman kotun a shekarar da ta gabata ya umarci jami’an tsaro da su daina hantarar wadanda ke zuwa kotun a yayin zaman shari'ar Kanu.

Ya ce jami’an tsaro na haifar da tashin hankalin da bai kamata ba saboda matakan da suke dauka.

A halin da ake ciki, an ga lauyoyi da masu ruwa da tsaki a harabar kotun da suka hada da lauyan Kanu, Aloy Ejimakor wanda ke jagorantar tawagar wasu lauyoyin da ke kare Kanu.

An kuma ga lauya ga babban hafsan soji, Amos Tory da sauran lauyoyin da ke tsagin gwamnati.

'Yan jarida daga manyan kafafen yada labarai na kasa da kasa ciki har da BBC su ma sun halarci wurin.

Daga cikin masu ruwa da tsakin har da Cif Ugo Chinyere, Igboayaka O Igboayaka, da sauran wasu da dama.

DSS ta yi watsi da umarnin kotu, ta kawo Nnamdi Kanu da kayan da ya saba zuwa kotu

A bangare guda daga Abuja, shugaban na IPOB, Nnamdi Kanu ya koma kotu yau Laraba da irin rigar da ya saba sakawa, lamarin da ya saba da umarnin mai shari’a Binta Nyako, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Nyako a yayin da ake ci gaba da shari’ar a ranar Talata ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta canzawa Kanu tufafi bayan da babban lauyansa, Cif Mike Ozekhome ya koka cewa ana gallaza masa a gidan yari.

A duk lokacin zaman kotu, ana ganin Kanu sanye tufafin Fendi kala daya tun lokacin da aka kamo shi a watan Yuni, 2021.

A lokacin da aka dawo kotu a yau Laraba, lauyan masu shigar da kara, Shuaibu Labaran, ya shaida wa kotun cewa Kanu ne ya zabi sanya kayan na Fendi ba tilasta masa aka yi ba.

A rahotonmu na baya kunji cewa, mai shari'a ta babbar kotun tarayya da ke Abuja, Binta Nyako, ta umurci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta bari Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar yan awaren IPOB da ya sauya kayayyakinsa.

A baya, Nyako ta umurci DSS da ta bari shugaban na IPOB ya dunga yin wanka a duk lokacin da yake son canja tufafinsa, ya ci abinci yadda ya kamata da kuma gudanar da addininsa.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa a zaman kotu na ranar Talata, 18 ga watan Janairu, Mike Ozekhome, lauyan Kanu, ya yi korafin cewa har yanzu wanda yake karewa baya samun kula mai kyau a hannun DSS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel