Gwamna mai jiran gado na shirin kafa kwamitin shirya Jarabawa da Intabiyu ga mutanen da zai naɗa

Gwamna mai jiran gado na shirin kafa kwamitin shirya Jarabawa da Intabiyu ga mutanen da zai naɗa

  • Ga dukkan alamu sai ka tsallake jarabawa da kuma Intabiyu ta baki da baki kafin ka shiga sabuwar gwamnatin jihar Anambra
  • Wasu alamu masu ƙarfi daga bakin makusantan gwamna mai jiran gado, Farfesa Soludo, na nuna za'a kafa kwamitin tantance waɗan da za'a naɗa
  • Hadimin zababben gwamnan yace suna samun matsin lamba kan kwamitin da zai shirya karban ragamar mulki

Anambra - Alamu masu ƙarfi sun bayyana a zahiri cewa gwamnan jihar Anambra mai jiran gado, Farfesa Charles Soludo, na shirin kafa kwamiti na musamman da zai gwada cancantar waɗan da zai naɗa a gwamnatinsa.

Punch ta rahoto cewa duk wani kwamishina ko wani naɗi da gwamnan ya yi, sai ya gurfana a gaban kwamitin, ya rubuta jarabawa kuma an masa Intabiyu baki da baki.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun zugo ‘Yan Majalisa su bankara Buhari a kan gyara dokar zabe

Hadimin zaɓaɓɓen gwamnan kuma shugaban ƙungiyar Anambra Leadership Forum, Mista Samuel Ejimofor, shi ne ya bayyana haka a Awka, ranar Litinin.

Zababben gwamnan Anambra, Farfesa Soludo
Gwamna mai jiran gado na shirin kafa kwamitin shirya Jarabawa da Intabiyu ga mutanen da zai naɗa Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Ya kuma shawarci mutanen dake kaiwa zababben gwamnan ziyara a mahaifarsa Isuofia dake karamar hukumar Aguata, suna neman shiga cikin waɗan da za'a naɗa, su dakata haka nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, zai fi kyau su shirya takardan bayanansu (CV) kuma su jira lokacin da za'a rantsar da sabon gwamnan da mutane suka zaɓa, bayan nan zai kafa kwmaitin naɗe-naɗe.

Yace:

"Ya kamata mutane su daina gaggawar zuwa rokon a basu wani muƙami, saboda tsohon tsarin da ake amfani da shi a baya, wani ya kawo ka, ya sa a baka muƙami ya wuce a yanzu."

Halin da ake ciki kan miƙa mulki a Anambra

Mista Ejimofor, ya ƙara da cewa suna fuskantar matsin lamba kan ƙara yawan mambobin kwamitin karɓan mulki daga mutum 80 zuwa 90 duba da ɗan lokacin da suke da shi.

Kara karanta wannan

Mun rage almubazzaranci, gwamnoni sun daina yawo cikin motoci 30, 40: Gwamna Badaru

"Game da kwamitin shirya karɓan mulki, lokacin ba shi da yawa idan ka duba abinda aka ɗora musu. Don haka duk masu ganin mun cika mutane a kwamitin to ba su san girman aikin dake kansu bane."
"Hakanan wasu kuma na ƙara matsa lamba cewa a ƙara yawan mambobin kwamitin zuwa 90 ko sama da haka."

A wani labarin kuma mun kawo muku abinda gwamna Masari ya gayawa Tinubu kan kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga a Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari, ya yi magana kan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka don kawo karshen matsalar tsaro yayin ziyarar Tinubu.

Masari yace gwamnatinsa ta fito da wani sabon tsarin tsaro da ya ƙunshi sarakuna, shugabannin addinai da sauran su a kowane ƙauye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel