Mun rage almubazzaranci, gwamnoni sun daina yawo cikin motoci 30, 40: Gwamna Badaru

Mun rage almubazzaranci, gwamnoni sun daina yawo cikin motoci 30, 40: Gwamna Badaru

  • Gwamna Badaru ya bayyana yadda gwamnoni ke rage kudaden da suke kashewa don tattalin arzikin jihohinsu
  • A cewarsa, maimakon yawo da motoci arba'in, yanzu Gwamnoni da motoci hudu suke fita
  • Gwamnan yace takwarorinsa yanzu sun fi mayar da hankali wajen samar da aiki ga jama'a

Abuja - Gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana cewa Gwamnonin Najeriya yanzu sun rage almubazzarancin da suke a baya da bannatar da kudaden gwamnati.

A cewarsa, Gwamnoni yanzu sun daina yawo cikin motoci 30 zuwa 40 kamar yadda suka saba.

Ya bayyana hakan ne a hirarsa da tashar ChannelsTV da daren Litinin.

Gwamna Badaru
Mun rage almubazzaranci, gwamnoni sun daina yawo cikin motoci 30, 40: Gwamna Badaru Hoto: Press COnference
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun tsaida matsaya kan zaben shugabanni da makomar Buni a taron Abuja

Ya ce shi da takwarorinsa Gwamnoni na iyakan kokari wajen rage kudaden da suke kashewa wajen gudanar da ofishohinsu.

A cewarsa:

"Dukkan Gwamnoni na neman hanyoyin rage kashe kudi. Ba zaka ga Gwamnoni na yawo cikin motoci 30 zuwa 40 ba. Yanzu cikin motoci uku zuwa hudu muke hawa."
"Yawancin Gwamnoni sun daina almubazzaranci don tattalin kudi."

Maimakon karban basussukan kudi, Gwamnan yace gwamnoni yanzu kokari suke wajen daukan ma'aikata a sashen Ilimi da kiwon lafiya.

Gwamnoni sun tsaida matsaya kan zaben shugabanni da makomar Buni a taron

A bangare guda, akalla gwamnoni 20 na jam’iyyar APC mai mulki suka yi zama a bayan labule a gidan gwamnatin jihar Kebbi da ke Asokoro, birnin Abuja.

Wani rahoton da Vanguard ta fitar ya ce ba a kammala wannan zaman a ranar Lahadi, 16 ga watan Junairu, 2022 sai da kimanin karfe 11:30 na dare.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya su rika yi mana adalci kan lamarin tsaro, muna kokari:Shugaba Buhari

Kan gwamnonin jam’iyyar mai mulki ya rabu a kan ko za a janye zaben shugabanni na kasa da aka tsara, ko kuwa zai wakana ne a watan na Fubrairu.

A karshen wannan taro, shugaban gwamnonin APC na kasa, Abubakar Atiku Bagudu ya ce kungiyarsu ta nuna goyon bayanta ga kwamitin Mala Buni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel