Gwamnonin PDP sun zugo ‘Yan Majalisa su bankara Buhari a kan gyara dokar zabe

Gwamnonin PDP sun zugo ‘Yan Majalisa su bankara Buhari a kan gyara dokar zabe

  • Gwamnonin jam’iyyar PDP sun shafe kimanin sa’a takwas su na yin wani taro na musamman a Ribas
  • A karshen wannan zama na jiya, gwamnonin jihohin adawar sun cin ma wasu matsayoyi da suka fitar
  • Kungiyar ta nemi majalisa ta maida kudirin zabe ya zama doka ko da shugaban kasa bai amince ba

Rivers - A daidai lokacin da ‘yan majalisa ke dawowa aiki bayan dogon hutun karshen shekara, sai aka ji gwamnonin jam’iyyar PDP sun yi zama a Fatakwal.

A karshen wannan taro da aka yi a jihar Ribas, gwamnonin jihohin adawa sun cin ma wasu matsaya. Jaridar The Guardian ta kawo rahoton abin da aka yi.

Daga cikin matsayar da gwamnonin jihohin hamayyar suka dauka shi ne ‘yan majalisa su yi fito na fito da shugaban kasa a kan batun kudirin gyara dokar zabe.

Kara karanta wannan

Zamfara: Matawalle ya ce suna shirin tona asirin masu aiki tare da ƴan ta'adda

A karshen zaman na ranar Litinin, gwamnoni 10 a cikin gwamnoni 13 na PDP sun sa hannu cewa bai dace Muhammadu Buhari ya yi watsi da kudirin gyara zabe ba.

Rahoton ya ce an dauki kusan awa takwas ana wannnan tattaunawa, inda kan gwamnonin ya hadu a cewar ‘yan majalisa su tursasa kudirin ya zama dokar zabe.

Wadannan gwamnoni sun ba ‘yan majalisar tarayya shawarar ka da su yarda da watsi da kudirinsu da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnonin PDP
Wasu Gwamnonin PDP Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Vanguard ta ce gwamnonin jihohin sun bukaci ‘yan majalisa su yi sauri su kammala zama a kan kudirin, su bankara shugaban kasa ko su yi wa kudirin garambawul.

Buhari na neman kawo cikas

A ra’ayin gwamnonin adawan, yin boren zai hana shugaba Buhari kawo cikas wajen gyara zabe.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Rikicin APC ya kara kamari, daraktan kungiyar gwamnoni ya yi murabus

Matsayar gwamnonin ya zo daidai da na tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, wanda yake ganin bai kamata ayi fatali da kudirin ba, duk da ya kunshi kura-kurai.

Haka zalika gwamnonin sun soki rikon da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ke yi wa sha’anin tsaro, su ka ce kusan kullum sai an zubar da jinanen ‘Yan Najeriya.

Yadda aka yi a taron

Gwamnonin da suka halarci taron da shugabansu, Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranta sun hada da Udom Emmanuel, Douye Diri da kuma Samuel Ortom

Sai Ifeanyi Okowa, Ifeanyi Ugwuanyi, Nyesom Wike, Seyi Makinde, Ahmadu Fintiri da Bala Mohammed da mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi Gusau.

Jaridar ta ce gwamna Godwin Obaseki da kuma Okezie Ikpeazu ba su samu halartar wannan taro ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel