Nasara Daga Allah: Sojoji sun aika yan bindiga lahira, sun kwato mutum 8 a Kaduna

Nasara Daga Allah: Sojoji sun aika yan bindiga lahira, sun kwato mutum 8 a Kaduna

  • Gwarazan sojojin Najeriya sun fatattaki yan bindiga daga yunkurin kai hare-hare wasu yankunan jihar Kaduna
  • Sojojin sun kuma samu nasarar hallaka yan ta'adda aƙalla uku yayin musayar wuta, sun kwato mutum 8 daga hannun su
  • Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya jinjinawa sojojin bisa nasarorin da suke samu a yaƙi da ta'addanci

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun kashe ɗan bindiga ɗaya, sun kubutar da mutum 8 daga hannun su a karamar hukumar Chikun.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, shi ne ya bayyana haka a wani rahoton tsaro da ya fitar a Facebook.

Haka nan kuma kwamishinan yace sojojin sun daƙile hare-hare a kananan hukumomin Giwa da Igabi, kuma sun aika wasu yan ta'adda lahira.

Kara karanta wannan

Kebbi: Rayuka 15 ne suka salwanta a farmakin ƴan ta'adda, Jami'ai

Sojan Najeriya
Nasara Daga Allah: Sojoji sun aika yan bindiga lahira, sun kwato mutun 8 a Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wane hari sojijin suka dakile?

Mista Aruwan ya bayyana cewa a bayanin da gwamnati ta samu daga hukumomin tsaro, sojojin sun kai ɗauki ga ƙarar harbe-harben da suka ji a Unguwan Musa dake Maraban Rido.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Yayin dogon musayar wuta da sojojin suka yi, sun ci ƙarfin yan ta'addan, waɗan da suka tsere ta cikin wani gini ɗauke da raunukan harbin bindiga, jinin da aka gani a jikin ginin ya tabbatar."
"Dakarun sojin ba su tsaya nan ba, suka shawo kan yan bindiga ta hanyar da suka yi nufin tserewa, a wannan matakin ne suka kubutar da mutum 8."
"Yayin musayar wuta da yan ta'addan, sojojin sun samu nasarar aika ɗaya daga cikin su zuwa wurin Ubangiji."

Kwamishinan ya bayyana sunayen mutanen da aka kubutar da, Likita Igah, Nancy Likita, Genesis Likita, Wilsom Likita, Mary Kalat, Victor Joel, Simon Musa Ali da kuma Rufus Elisha.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan Sojojin Najeriya sun yi doguwar musayar wuta da yan bindiga a Kaduna

Kazalika, sojojin sun dakile yunkurin harin yan bindiga a Hayin Kanwa dake karamar hukumar Giwa, inda suka kashe ɗan bindiga ɗaya, inji Aruwan.

Malam El-Rufa'i ya yaba wa sojojin

Bayan samun wannan rahoton, gwamna El-Rufa'i, ya nuna tsantsar farin cikinsa da yabo ga dakarun soji bisa wannan nasara.

Daga nan kuma ya mika sakon murna da fatan alkairy ga mutum takwas da sojojin suka kubutar daga hannun yan ta'adda.

A wani labarin na daban kuma Amarya da Ango sun rasa rayuwarsu lokaci daya makonni bayan baikon auren su

Wani saurayi da budurwarsa dake shirin zama Ango da Amarya sun rasa rayuwarsu lokaci ɗaya makonnin bayan amince wa zasu yi aure.

Masoyan biyu, Ma'aikatan jinya ne da suka yi aikin neman kwarewa a cibiyar lafiya ta tarayya dake jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel