Lokaci: Amarya da Ango sun rasa rayuwarsu lokaci daya makonni bayan baikon auren su

Lokaci: Amarya da Ango sun rasa rayuwarsu lokaci daya makonni bayan baikon auren su

  • Wani saurayi da budurwarsa dake shirin zama Ango da Amarya sun rasa rayuwarsu lokaci ɗaya makonni bayan amince wa zasu yi aure
  • Masoyan biyu, Ma'aikatan jinya ne da suka yi aikin neman kwarewa a cibiyar lafiya ta tarayya dake jihar Adamawa
  • Kareem Oluwagbemiga, da Amaryarsa Usulam Enoch, sun rasu ne a wani hatsarin mota a hanyar Jos zuwa Abuja

Wani ma'aikacin jinya a Najeriya (Nurse), Kareem Oluwagbemiga, da budurwarsa wacce suka amince da auren juna, Usulam Enoch, sun rasa rayuwarsu lokaci ɗaya.

Matasan biyu dake shirin zama Amarya da Ango sun rasu ne yayin da wani mummunan hatsari ya rutsa da su a kan hanyar Jos zuwa Abuja.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Nurses On Air suka fitar a shafinsu na dandalin sada zumunta Facebook, ranar Talata, yayin da suke jajanta wannan rashi da suka yi.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi shigar soji, sun dauke ‘yan biki, sun bukaci a biya fansar Naira Miliyan 60

Saurayi da Budurwa
Tashin Hankali: Amarya da Ango sun mutu lokaci ɗaya makonni bayan saka ranar Aurensu Hoto: Kareem Oluwagbemiga
Asali: Facebook

Sanarwan tace:

"Babban abun takaici ne da alhini da muka samu labarin rasuwar abokin aikin mu, Nas Kareem Oluwagbemiga, tare da budurwarsa, wacce suka amince da Auren junan su."
"Baki ɗayansu sun rasa rayuwarsu ne bayan wani hatsarin mota ya rutsa da su a kan hanyar Jos-Abuja. Wannan babban rashi ne a aikin jinya."
"Muna addu'a, Allah mai girma ya baiwa iyalansu da kuma bangaren aikin jinyar marasa lafiya hakurin wannan babban rashi."

Yaushe masoyan suka amince da yin aure?

Oluwagbemiga, ya amince da auren budurwarsa a ranar 6 ga watan Disamba, 2021, iyalai da abokan arziki sun samu halartar wannan shagali.

Hotunan wannan shagali na nan a shafin Facebook na Oluwagbemiga, wanda yanzu yan uwa ke ɗauka suna nuna alhini da jimamin rasuwar matasan biyu.

Kara karanta wannan

An kashe mutane 5, an kona gidaje sakamakon arangama tsakanin makiyaya da manoma a Ogun

Kafin mutuwarsu, Oluwagbemiga da matar da zai aura, sun yi aikin neman kwarewa a aikin jinya a Cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya dake Yola, jihar Adamawa.

A wani labarin na daban kuma Kotu ta yanke wa wani tsohon Sojan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar Rataya

Wata babbar kotu a jihar Ekiti ta yanke wa korarren tsohon sojan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar Rataya bayan samunsa da laifi.

Alkalin kotun ya bayyana cewa kotu ta samu mutum biyun da laifin aikata fashi da makami kan wani mai gidan man fetur a Ado-Ado, jihar Ekiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel