Ba zan taba sukar Tinubu ba, aboki na ne: Orji Uzor Kalu

Ba zan taba sukar Tinubu ba, aboki na ne: Orji Uzor Kalu

  • Orji Uzor Kalu ya yi watsi da maganganun cewa ya zagi tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu
  • Sanata Kalu ya ce Tinubu abokinsa ne na kwarai kuma babu abinda zai sa ya zagesa
  • Shahrarren dan siyasa, Ahmed Tinubu, ya bayyana niyyar zama magajin Tinubu a 2023

Tsohon Gwamnan jihar Abia kuma mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya wanke kansa daga rahotannin cewa yana zagin jagoran All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu.

Zaku tuna cewa Kalu a wata hirar da yayi ya ce shirya yake da ya 'kara da Tinubu a zaben fidda gwanin kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Martani kan rahotannin cewa ya zagi tsohon gwamnan jihar Legas, Kalu ya yi magana ta ofishin yada labaransa inda yace:

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

"Ba zamu taba sukar Tinubu ba"
"Na fadawa yan Najeriya cewa zan yi takara da Tinubu idan aka baiwa yankin kudu tikici. APC jam'iyyar demokradiyya ce dake baiwa kowani mamba da ya cancanta daman zabe kuma a zabesa."
"Ba jam'iyyar wani mutum daya bace. Idan nace zan yi takara da Tinubu, hakan bai nufi na zageshi. Ba zan iya zaginsa dan wani dalili ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba zan taba sukar Tinubu ba, aboki na ne: Orji Uzor Kalu
Ba zan taba sukar Tinubu ba, aboki na ne: Orji Uzor Kalu
Asali: UGC

"Abin takaici ne wani yan tsiraru na kokarin juya maganata don wata manufa ta siyasa."

"Ko kadan ban damu ba. Abota na da Tinubu mai zurfi ne kuma ba na fada da shi. Ban adawa da niyyarsa na zama shugaban kasa. Jam'iyya ce zata zabi dan takararta," tsohon gwamnan ya kara.

Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Sanata

Kara karanta wannan

Idan har Tinubu ya zama Shugaban kasa zan bar Najeriya, Bode George ya lashi takobi

Ba zamu sake kuskuren zaben mutum irin Buhari ba, Dattawan Arewa

A wani labarin kuwa, kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa yankin Arewa zata zabi dan takaran shugaban kasa mai ikon sauya lamuran tattalin arzikin kasar da tsaro ba tare da la'akari da yankin da ya fito ba.

Dattawan sun ce ba zasu sake zaben dan takara bisa kabilanci kamar yadda suka zabi Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 ba.

Dattawan sun bayyana cewa Shugaba Buhari abin kunya ne ga Arewa da Najeriya gaba daya.

Kaakin kungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana hakan ne yayin ganawar dattawan arewa a jihar Kaduna ranar Asabar, rahoton ChannelsTV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel