Ba zamu sake kuskuren zaben mutum irin Buhari ba, Dattawan Arewa

Ba zamu sake kuskuren zaben mutum irin Buhari ba, Dattawan Arewa

  • Dattawan Arewa sun ce a 2023 mutumin da zai yi aiki zasu zaba ko da ko ba dan yankin Arewa bane
  • Dattawan sun hadu a Arewa House dake jhar Kaduna don tattauna matsayar yankin gabanin zaben 2023
  • Game da ikirarin da yankin Igbo ke yi na cewa dole a basu tikitin shugaban kasa, dattawa sun ce wannan ba magana bane

Gabanin zaben 2023, kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa yankin Arewa zata zabi dan takaran shugaban kasa mai ikon sauya lamuran tattalin arzikin kasar da tsaro ba tare da la'akari da yankin da ya fito ba.

Dattawan sun ce ba zasu sake zaben dan takara bisa kabilanci kamar yadda suka zabi Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 ba.

Dattawan sun bayyana cewa Shugaba Buhari abin kunya ne ga Arewa da Najeriya gaba daya.

Kara karanta wannan

Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba

Ba zamu sake kuskuren zaben mutum irin Buhari, Dattawan Arewa
Ba zamu sake kuskuren zaben mutum irin Buhari, Dattawan Arewa Hoto: ChannelsTV
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kaakin kungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana hakan ne yayin ganawar dattawan arewa a jihar Kaduna ranar Asabar, rahoton ChannelsTV.

Yace yaudararsu akayi su zabi Shugaba Buhari saboda ana sa ran cewa zai gyara kasar.

Ya ce amma abin takaici, abubuwan sun gurbace Arewa da Najeriya gaba daya fiye da lokacin da Shugaba Buhari ya hau mulki a 2015 saboda garkuwa da mutane da talauci sun zama ruwan dare.

Baba Ahmed yace a baiwa Arewa da Kudu daman gabatar da yan takara maimakon cewa dole sai dan kudu zai yi takara.

Ku dakatad da shirin kididdigan yan kasa

Dattawan Arewa sun yi kira da Gwamnatin tarayya ta dage shirin kididdigan yan kasa da take yi saboda akwai yan gudun hijra da dama a fadin tarayya kuma hakan zai yi iya tada rikici yayinda ake shirin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Addini, rashin lafiya, da matsaloli 5 da Tinubu zai fuskanta a neman Shugaban Najeriya

Hakazalika sun yi kira ga Gwamnati ta sauya dokar zabe kuma Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan dokar da aka yiwa gyara kafin zabe.

Yan Najeriya su rika yi mana adalci kan lamarin tsaro, muna kokari: Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi iyakan kokarinta wajen magance ta'addanci amma ba za suyi kasa a gwiwa ba.

Hakazalika ya yi kira ga yan Najeriya su yiwa gwamnatinsa adalci idan suna magana kan lamarin tsaro dubi ga yadda ya samu kasar a 2015 lokacin da ya hau mulki.

A cewarsa, Gwamnatinsa ta samu nasarori da dama musamman a yankin Arewa maso gabas da Kudu maso kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel