‘Yan bindiga sun yi shigar soji, sun dauke ‘yan biki, sun bukaci a biya fansar Naira Miliyan 60

‘Yan bindiga sun yi shigar soji, sun dauke ‘yan biki, sun bukaci a biya fansar Naira Miliyan 60

  • Ana zargin ‘yan bindiga sun dauke wasu mutane bakwai a hanyar dawowa daga biki a garin Ibadan
  • Miyagun sun saki mutum 3 da nufin su nemo Naira miliyan 60 domin a saki sauran abokan tafiyarsu
  • Wani daga cikin wadanda yanzu ya kubuta ya ce an tare su ne a babban titin Legas zuwa garin Ibadan

Ogun - Wasu ‘yan iskan gari da suka yi shiga tamkar jami’an sojojin kasa, sun dauke mutane bakwai da ke dawowa daga bikin daurin aure a Isara, jihar Ogun.

Jaridar Punch ta ce an dauke wadannan Bayin Allah ne a kan hanyar Legas zuwa garin Ibadan.

Rahoton ya ce mutanen da aka sace su na hanyar dawowa gida ne daga wajen biki da aka yi a garin Ibadan, jihar Oyo a ranar Asabar, 16 ga watan Junairu, 2022.

Kara karanta wannan

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

Matafiyan sun fada tarkon miyagun ne yayin da motarsu ta lalace a kan titin na Legas-Ibadan. Ana kokarin a janye motarsu ne sai ga masu garkuwa da mutanen.

An fito da mutane uku

Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da shi, Folahan Akinsola ya shaidawa manema labarai cewa su na shirin jan motar abokin tafiyarsu ne aka kama su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikin mutane bakwai da aka kama, Folahan Akinsola ya ce an saki mutane uku (har da shi). ‘Yan bindigan sun bukaci a biya N60m kafin a fito da ragowar.

Highway Road
Titin Legas zuwa Ibadan Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Akinsola ya ce wadanda suka dauke su zuwa cikin jeji, sun yi shigar sojoji ne. Duk da ya tsira, wannan Bawan Allah ya ce miyagun sun karbe masu dukiya.

Yadda abin ya wakana

“Ina cikin wadanda aka saki su tafi su nemo N15m da za a fito da sauran mutanen hudu. Yanzu mu na bukatar N60m, shiyasa mu ke neman taimako.”

Kara karanta wannan

An kuma: An sake yin garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato

“Masu garkuwa da mutanen sun ce za su kashe ragowar mutanen idan ba mu samo kudin ba.”
“Bayan mun kubuta, mun kira 911. A hanyar komawa Ibadan inda mu ka hadu da ‘yan sanda, mun sanar da su, amma aka ce mu tuntuni ‘yan sandan Isara.”

- Folahan Akinsola

Za a kashe su idan babu N60m

“Mun kai kara a can, mu ka kuma samu labari cewa DPO ya aika dakaru 25 su tsare yankin. ‘Yan bindigan su na ta turo mana bidiyon ‘yanuwan mu a tsare.”

An bada sunayen wadanda ke tsare da Adeola Bude, John Segun, Demola, da wani mai suna Shola kamar yadda wani ya nuna hotuna da bidiyo a shafinsa na Twitter.

Tasrin COVID-19

Oxfam ya bayyana cewa daga farkon 2020 zuwa yau, dukiyar wasu manyan masu kudin kasar nan ta karu da kusan Dala biliyan 7 yayin da ake fama da COVID-19.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai

A daidai wannan lokaci kuma talakawa sun kara yawa da akalla mutane miliyan 7.4, mafi yawan mutane sun shiga halin ha’ula’i a dalilin annobar cutar Coronavirus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel