Kotu ta yanke wa wani tsohon Sojan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar Rataya

Kotu ta yanke wa wani tsohon Sojan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar Rataya

  • Wata babbar kotu a jihar Ekiti ta yanke wa korarren tsohon sojan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar Rataya
  • Alkalin kotun ya bayyana cewa kotu ta samu mutum biyun da laifin aikata fashi da makami kan wani mai gidan man fetur
  • Mai Sharia, Lekan Ogunmoye, yace kotu ta samu kwararan hujjoji da suka wuce tantama akai daga hannun masu gabatar da ƙara

Ekiti - Wata babbar kotu dake Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, ranar Litinin, ta yankewa Damilola Olasoji, tsohon sojan Najeriya da aka sallama daga aiki, da kuma Koiki Benson, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Premium Times ta tattaro cewa kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin ne bisa kama su da aikata laifin fashi da makami.

Hukuncin rataya
Kotu ta yanke wa wani tsohon Sojan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar Rataya Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yan sanda sun shaida wa kotun cewa a ranar 30 ga watan Maris, 2016, Olasoji, Benson da kuma Ogbesetuyi Tunde, suka haɗa kai suka farmaki Oluwadare Adebayo a gidan mai dake Ado-Ado, suka saci miliyan N1.2m.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mutane sun shiga daji sun kwato Sarkin su da yan bindiga suka sace a Filato

Yadda Kotu ta yanke hukuncin

Da yake yanke hukuncin, Mai shari'a Lekan Ogunmoye, yace masu gabatar da ƙara sun kafa hujjoji da suka zarce kokanto kan waɗan da ake zargi cewa sun aikata laifin da ake tuhumar su.

Alkalin kotun, ya yanke wa ɗaya daga cikinsu, Mista Tunde, hukuncin ƙare ragowar rayuwarsa a gidan gyaran hali.

Daily Trust ta rahoto Alƙalin Yace:

"A tuhuma ta biyu, abin da ya shafi fashi da makami, kotu ta yanke wa Olasoji da kuma Benson hukuncin kisa ta hanyar rataya. Allah ya gafarta wa ransu."

Yadda mutanen suka aikata fashi da makami

Da yake bada shaidar abinda ya faru, Mista Adebayo, wanda aka yi wa fashin, ya shaida wa kotu cewa da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, mutanen suka zo gidan mansa suka yi kamar sun zo siyan man fetur ne.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da 1.5m da za a kai Kebbi da Kano

"Sun tilasta shiga babban ofishin mu, kuma suka sharara mun mari. Bayan haka suka cigaba da duka na lokaci zuwa lokaci da kan bindiga."

A wani labarin na daban kuma Kaftin Hassan, wani Gwarzon sojan Najeriya da ya hallaka dandazon mayakan Boko Haram shi kaɗai

Akwai dakaru da dama a rundunar sojojin Najeriya da suka bada gudummuwa wajen yaƙi da ta'addanci fiye da tsammani amma ba kowa ya san su ba.

Mun tattaro muku takaitaccen bayani kan Kaftin Hassan, sojan da shugaban Boko Haram yasa kyautar miliyan N10 ga duk wanda ya kashe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel