An tsinta gawar magidanci mai shekara 41 a otal, an cire wasu sassan jikin sa

An tsinta gawar magidanci mai shekara 41 a otal, an cire wasu sassan jikin sa

  • An tsinta gawar magidanci Azubuike Nwokolo, wanda aka fi sani da Zubby More mai shekaru 41 a wani otal da ke Amichi a Nnewi
  • 'Yan uwan mamacin sun ce akwai abinda ake boye musu kan mutuwarsa domin sun duba gawarsa sun ga an cire masa 'ya'yan maraina
  • Hukumar otal din ta ce fadi ya yi a bandaki kuma ya mutu, duk da cewa wasu mutane da ba a sani ba ne suka sanar da 'yan uwansa ya na mutuware

Anambra - Wani magidanci mai shekara arba'in da daya mai suna Azubuike Nwokolo wanda aka fi sani da Zubby More, an tsinta gawarsa a dakin otal da ke Amichi, karamar hukumar Nnewi ta arewa a jihar Anambra, babu wasu daga cikin sassan jikin sa.

Daily Trust ta tattaro cewa, magidancin mai 'ya'ya biyu ya halarci liyafa ne a yankin a ranar 13 ga watan Janairu kuma ya yanke hukuncin kwana a otal din saboda dare ya yi kuma ba zai iya zuwa gida ba.

Kara karanta wannan

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

An tsinta gawar magidanci mai shekara 41 a otal, an cire wasu sassan jikin sa
An tsinta gawar magidanci mai shekara 41 a otal, an cire wasu sassan jikin sa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daya daga cikin abokan mamacin mai suna Nnaemeka Ikerionwu, wanda ya bukaci a bi khadin mamacin, ya ce an samu gawar sa a dakin otal da ke Amichi, jihar Anambra.

“Ya je wata liyafa ne kuma dare ya yi masa ta yadda ba zai iya zuwa gida ba. Hakan yasa ya kwana a otal da ke Amichi a jihar Anambra. Bai dawo gida ba, hakan ya gigita iyalan sa," Ikerionwu yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito cewa, kamar yadda yace, bayan bai dawo ba, an fara neman sa kuma an samu gawar sa a dakin otal din.

Ya ce ko a lokacin da hukumar otal din suka yi ikirarin cewa yanke jiki ya yi ya fadi ya mutu, ba su tuntubi iyalansa ko 'yan sanda ba kafin su kai shi ma'adanar gawawwaki.

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

Ikerionwu ya ce, "wasu mutane da ba a sani ba ne suka sanar da iyalan cewa dan su ya mutu kuma ya na ma'adanar gawawwaki. Sun je ma'adanar kuma sun samu cewa an cire 'ya'yan marainan sa. Sun fuskanci ma'aikatan otal din amma sun ce fadi ya yi a bandaki kuma ya mutu.

Ya kara da cewa, iyalan mamacin sun zargi cewa, akwai lauje cikin nadi saboda sun ga raunika a jikin mamacin.

Kamar yadda yace, 'yan uwa da abokan sa suna kira ga rundunar 'yan sandan jihar Anambra da su duba lamarin tare da tabbatar da cewa an yi masa adalci.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, DSP Toochukwu Ikenga, ya ce ba shi da masaniya kan lamarin.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon kakakin majalisa, Duruji

A wani labari na daban, masu garkuwa da mutane sun sace tsohon kakakin majalisar jihar Imo, Lawman Duruji, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka fatattaki babban abokin ango daga wurin ɗaurin aure saboda gemunsa ya janyo cece-kuce

Wakilin Punch ya tattaro bayanai akan yadda aka sace Duruji a karamar hukumar Ehime Mbano ranar Asabar a Oriagu yayin da ya ke dawowa daga wani taro.

Sun kuma yi garkuwa da wani dan kasuwa a Owerri, wanda aka fi sani da Ezzybee. A ranar Lahadi aka sace Ezzybee a hanyarsa ta zuwa wurin kallon kwallo.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel