Bidiyon yadda aka fatattaki babban abokin ango daga wurin ɗaurin aure saboda gemunsa ya janyo cece-kuce

Bidiyon yadda aka fatattaki babban abokin ango daga wurin ɗaurin aure saboda gemunsa ya janyo cece-kuce

  • An fatattaki babban abokin ango ranar auren abokinsa daga cikin coci duk saboda gemunsa
  • Matashin ya nuna mamakinsa a kan yadda lamarin ya auku saboda hakan bai taba faruwa ba
  • ‘Yan Najeriya da dama sun dinga cece-kuce akan irin tozarcin da cocin ta yi masa, hakan ba daidai bane ga bako

Jihar Abia - Wani dan Najeriya ya koka a kan yadda aka fatattake sa daga wurin wani biki a cikin coci saboda gemunsa, Legit.ng ta ruwaito.

A cewar mutumin wanda bai bayyana sunansa ba, shi ne babban abokin ango, ya halarci daurin auren abokinsa sai kuma aka kore shi.

Bidiyon yadda aka fatattaki babban abokin ango daga wurin ɗaurin aure saboda gemunsa ya janyo cece-kuce
An fattaki babban abokin ango daga wurin daurin aure a coci saboda gemunsa. Hoto: @instablog9ja Source: Instagram
Asali: Instagram

Kara karanta wannan

Ba motar hawa suke da shi ba sai yawan tambaya game da gadar sama da na ke gina wa, Ikpeazu ya mayar da martani

Ya ce lamarin ya yi matukar ba shi mamaki. Kuma bai taba tunanin hakan zai faru da shi ba.

A wani bidiyo wanda aka yi a harabar coci tare da wata budurwa, abokin angon ya ce lamarin ya auku ne a Redeemed Christian Church of God, RCCG, da ke Aba, Jihar Abia.

A bidiyon wanda ya yi cike da mamaki, mutumin ya ce hakan bai taba faruwa ba ko da kuwa a sauran rassan cocin da ke wasu bangarorin na kasa.

Daga sautin da ke tashi, alamu na nuna cewa an ci gaba da shagalin bikin duk da an kori abokin angon.

‘Yan Najeriya sun hau caccakar cocin

Nan da nan mutane su ka je karkashin bidiyon su ka dinga caccakar cocin akan irin rashin kyautawar da su ka yi.

@iam_lonwolf ya ce:

“A jininsu hauka take. Ya ce musu yana son bayar da sadakar miliyan daya a cocin. Za su baza masa kafet mai kyau ne.”

Kara karanta wannan

Martanoni da ra’ayoyin mutanen Facebook game da burin Tinubu na zama Shugaban Najeriya

@tolatayo ya ce:

“Ya kamata cocin su gane cewa bakon ba cikinsu ya ke ba, kada su kallafa wa bako dokarsu..”

@blackvelvete ta yi tsokaci da:

“Na tuna wani biki da mu ka je coci irin wannan, sun dakatar da ni daga shiga saboda rigata tana da tsagu.”

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel