Mazan Jiya: Filin yaƙi Mbormi inda tsohon Sultan Attahiru ya mutu yayin kare Martabar Musulmai daga Turawa

Mazan Jiya: Filin yaƙi Mbormi inda tsohon Sultan Attahiru ya mutu yayin kare Martabar Musulmai daga Turawa

  • Sheikh Usman Ɗan Fodio, babban malami ne da musulmai ba zasu mance da jihadinsa ba a Najeriya har ya kafa masarautar Musulmai a Sokoto
  • Sai dai Khalifa na 12 bayan rasuwar Ɗan Fodio, Sultan Attahiru. ya rasa rayuwarsa ne a kokarin kare martabar Masarautar kakansa
  • Mun tattaro muku bayanai kan filin yaƙin Mbormi, wanda Sultan Attahiru II ya rasu yayin fafatawa da turawan mulkin mallaka

Sultan suna ne da ake kiran Sarkin Musulmai, babbar fadarsa na jihar Sokoto. Kalipha ko muce Sarkin Musulmi na farko, Sheikh Usman Dan Fodio, shine ya kafa masarautar.

Masarautar na da manyan rassa a Arewacin Najeriya, waɗan da ke karkashin mulkinta domin ita ce cibiyar gwamnatin Musulunci da Ɗan Fodio ya kafa bayan jihadi a 1804.

Leadership ta ruwaito cewa, Sarakuna 11 ne suka jagoranci Masarautar bayan wafatin Sheikh Fodio, kafin turawan mulkin mallaka su ƙwace iko da Masarautar bayan kafa gwamnati.

Sarakunan, waɗanda suke tsatsan Ɗan Fodio sun haɗa da, Muhammad Bello, Abubakar Atiku, Ali Babba Bn Bello, Ahmadu Atiku, Aliyu Karami, Ahmadu Rufa’i, Abubakar Atiku II, Malam Muazu, Umar Bn Ali, Abdulrahman Dan Abubakar, Muhammad Attahiru I da Sultan Attahiru II.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu

Sarki Attahiru
Mazan Jiya: Filin yaƙi Mbormi inda tsohon Sultan Attahiru ya mutu yayin kare Martabar Musulmai daga Turawa Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Sultan Attahiru II, shi ne Sarkin Musulmi na ƙarshe da ya jagoranci Masarautar kafin dakarun turawan mulkin mallaka su samu galaba kan Masarautar, suka maida ta ƙarƙashin su.

Ya rasu ne a shekarar 1903 a filin yaƙin Mbormi dake Bajoga, ƙaramar hukumar Funakaye a jihar Gombe.

Ina ne filin yaƙin Mbormi?

Mbormi, shi ne wurin da dakarun turawa suka rutsa Sarkin Musulmi na 12 tare da sojojinsa a kokarin su na kwace yankin ƙasar Hausa.

Gwamnatin turawan mulkin mallaka ta haɗa yankin Arewaci da Kudancin ƙasar nan a matsayin ƙasa ɗaya a shekarar 1914.

Sai dai duk da haka, ba abu ne mai sauki turawan su kwace yankin ƙasar Hausa ba domin dole ne su fafata a fagen yaƙi da Masarautar Sarkin Musulmi.

An fafata yaƙi tsakanin Sultan na wancan lokacin, Attahiru na II da kuma sojojin Turawa, a filin Mbormi, inda Attahiru wanda ya yi ƙoƙarin kare Masarautar Mulsulmai da kwamandan sojojin Turawan Burtaniya suka mutu a yaƙin.

Kara karanta wannan

Na-kusa da Turji ya fallasa asirin inda ‘Dan bindigan ke samun makamai da taimako

Sarki Attahiru ya jagoranci Masarautar daga watan Oktoba, 1902, zuwa watan Maris, 1903. Kuma shi ne Sarki na ƙarshe kafin mamaye Masarautar.

Abin da ya faru bayan kwace Masarautar Musulmai

Tun daga wannan lokaci ne gwamnatin Turawan mulkin mallaka ta maida Sarakunan wannan babbar Masarauta yan amshin shata.

Gwamnati ta koma amfani da sarakuna wajen isar da dokokinsu ga mutane, inda suka mayar da duk wani Basarake ɗan amshin shata, sai abin da suka ga dama za'a yi.

Wakilin jaridar Leadership ya tattaro cewa tun bayan kashe Sultan Attahiru a filin yaƙin Mbormi, mutane suka maida wurin ya zama abin tunawa da mazan jiya.

Hakan ta faru ne saboda wurin na ƙunshe da ƙabarin Sarki Attahiru, da kuma kwamandan dakarun Burtaniya da kuma sojojin su.

A cewar ma'aikatar labarai da al'adu ta jihar Gombe, filin yaƙin Mbormi, yana da daraja, ƙima, tarihi da kuma muhimmanci a ƙasa baki ɗaya.

Hakanan kuma, ya zama wurin dake jawo hankalin mutane su kai ziyara domin tunawa da Mazan Jiya, waɗanda suka jajirce har suka yi Shahada a fagen fama.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani kan kyautar da Tinubu ya bayar na N50n ga 'yan Zamfara

A rahoton bikin al'adu na shekarar 2017 a jihar Gombe, wanda Aliyu Abdu da Dipo Alafiatayo, suka tattara, ya nuna cewa gwamnatin jiha ta ɗauki wurin da matuƙar muhimmanci.

Har zuwa yanzun, akwai ɓurɓushin alamar ƙabarin kwamandan Turawa a wurin, amma ƙabarin Sarki Attahiru, da babban limaminsa an killace su.

Abin da gwamnatin jihar Gombe ta yi

Wakilin mu ya gano cewa gwamnatin jihar Gombe da ta shuɗe ƙarƙashin gwamna Ibrahim Dankwambo, ta fara aikin gyara filin yaƙin Mbormi, domin ya zama wurin kai ziyara, amma aikin ya tsaya bayan shuɗewar wa'adinsa.

Gwamnatin baya a jihar ta yi yukurin killace filin da katanga, ta gina masallaci, ɗakin bincike da sauran su domin jawo hankalin masu yawon buɗe ido.

Me mutane ke cewa game da Mbormi?

Wasu mazauna jihar Gombe da suka zanta da wakilin Leadership, sun bayyana cewa, mutanen yanzu da dama ba su san tarihin wannan filin yaƙi ba.

Kara karanta wannan

Ya'yan tsohon shugaban sojojin Najeriya sun maka kawunsu a gaban kotu kan dukiyar gado

Ɗaya daga cikinsu, Malam Hassan Tijjani, yace matukar aka ƙara gyara wurin, zai taimaka wa mutane musamman matasan yanzun sanin tarihin filin.

Ya kara da cewa, bayan jawo hankalin masu buɗe ido da filin yaƙin zai yi, zai kuma ƙara wa garin Bajoga suna, domin mutane daga kowane yanki za su rinka zuwa yawon buɗe ido.

Ya shawarci gwamnati bayan ta zamanantar da wurin, kuma ta yi kasuwanci da shi da nufin ƙara yaɗa shi a duniya.

Shin gwamnatin Gombe na da shirin gyara Mbormi?

Da aka tambaye shi ko gwamnatin Gombe ta yanzun na da wani shiri a ƙasa na gyara filin yaƙin Mbormi, kwamishinan labarai da al'adu, Julius Ishaya Lepes, ya ƙi cewa komai kan lamarin.

Amma Filin yakin Mbormi, na ɗaya daga cikin wurare 5 da aka bada shawarar saka su a cikin tarihin Musulmai na duniya tare da Hubbaren Ɗan Fodio.

A wani labarin kuma ASUU zata maka gwamna El-Rufa'i a gaban kotu kan abinda yake shirin yi wa jami'ar ABU Zaria

Kara karanta wannan

Muruwa rigar kowa: Shugaban karamar hukuma ya yanke jiki ya fadi, ya cika a Asibiti

Kungiyar ASUU reshen jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, (ABU) ta gargaɗi Elrufa'i ya dakatar da kudirinsa kan filayen jami'a.

Shugaban ASUU-ABU, Farfesa Nasiru, yace kungiyarsu ba zata naɗe hannu tana kallo a yi wa jami'a ƙarfa-ƙarfa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel